Gwamnan jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang ya amince da fara aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikata a jihar nan take.
Amincewar ta biyo bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar da kwamitin ya yi kan daidaita albashin a ranar Laraba 13 ga Nuwamba, 2024.
- Cire Tallafin Man Fetur Ya Kawo Ƙarshen Fasa-ƙwauri, in ji NSA
- Nijeriya Na Buƙatar Maki 3 Yau Domin Samun Gurbi A Gasar Ƙasashen Afrika
A wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar, Stephen Gadong ya fitar, ya ce aiwatar da sabon albashin ya nuna kudirin gwamnati na ba da fifikon jin dadin ma’aikatanta wajen amincewa da gagarumar rawar da suke takawa wajen ciyar da manufofin ci gaban gwamnati.
Gadong ya karfafa gwiwar ma’aikatan gwamnati da su rungumi wannan karimcin ta hanyar sake jajircewa wajen gudanar da ayyukansu tare da sabunta kwazo da himma wajen sauke nauyin da ya rataya akansu da nagarta a jihar