An tabbatar da mutuwar mutum guda yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon haɗarin mota da ya faru a gadar Nyanya, Abuja, lokacin da birkin wata babbar mota (trailer) ya ƙi aiki, hakan yasa ya kutsa wasu motoci.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta babban birnin tarayya (FEMD) ta tabbatar da cewa waɗanda suka jikkata suna samun kulawa a Asibitin ƙasa da ke Abuja.
- An Cafke Mai Garkuwa Da Mutane A Sansanin Alhazan Abuja
- ‘Yansanda Sun Nemi A Kwantar Da Hankula Bayan Fashewar Wani Abu A Abuja
Shugaban FEMD na riƙon ƙwarya, Injiniya Abdulrahman Mohammed, ya bayyana cewa an miƙa gawar matashin da ya rasu ga iyalansa ta hannun hukumar Ƴansandan FCT da kuma sashin ceto na FEMD.
Mohammed ya bayyana cewa waɗanda hatsarin ya rutsa da su ‘yan uwa ne a gida ɗaya kuma suna tsaye a bakin hanya lokacin da hatsarin ya faru.
“Hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 6:30 na yamma lokacin da wata motar Coca-Cola ta birki ya twinkle, ta bugi motoci da dama kafin ta ƙara buge wata motar kamfanin gine-gine. Direbobin dukkan motocin sun tsira ba tare da rauni ba. Haka zalika, wata jami’ar Kwastam da motarta ta ke cikin hatsarin ba ta samu rauni ba,” inji shi.
Ya ce jami’an FEMD, FRSC da ‘yansanda sun gaggauta zuwa wurin domin gudanar da aikin ceto. Mohammed ya ja kunnen direbobi da su tabbatar motocinsu na cikin ƙoshin lafiya kafin su hau hanya.
Ya kuma shawarci jama’a da su rika kiran lambar gaggawa 112 idan wani lamari ya faru. Wannan hatsari ya ƙara tayar da hankali kan lafiyar hanyoyi, inda hukumomi ke kira da a dunga bin dokokin kula da lafiyar motoci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp