Akalla mutane 10 ne aka ruwaito cewa sun mutu, inda wasu kuma da dama, aka kwantar da su a asibiti bayan da suka sha shayin gadagi wanda ake zargin an hada shi ne da wani ganyen shayin Zakami.
Mutanen sun sha shayin ne, a taron wani biki a Jihar Kano.
- Buhari Ya Nada Sabon Mai Ba Da Shawara Kan Sha’anin Tsaro
- Ma’aikatan Filato Sun Fara Yajin Aiki Kan Rashin Biyan Su Albashi
Zakami dai, na dauke da wani sanadarin da ke sanya wa wanda ya sha kuzari.
Lamarin ya auku ne a ranar Talata a unguwar Sheka da ke a karamar hukumar Kumbotso a Jihar Kano.
Daya daga cikin ganau, Sanusi Yahaya wanda kuma babban yaya ne ga amaryar da aka daura wa auren, ya bayyana cewa, ana zargin ana hada shayin da kwaya da kuma ganyen Zakamin.
Ya ce, abin kusan ya zama jiki, musamman ga masu ta’ammali da kayan maye da ke yin amfani da shi a lokacin bukukuwa.
A cewarsa, suna dafa shayin kuma ba su san adadin kwayar da ke cikin shayin ba, inda hakan ya sa wasu suka yi watsi da shayin wasu kuma suka matsa sai sun sha shayin bisa cewarsu kwakwalwarsu za ta iya dauka.
Ya ci gaba da cewa, bayan sun sha shayin ne, sai mutum biyu suka fara mutuwa, wasu kuma suka farfado, inda kuma garzaya da wasu asibiti.
Shi ma wani ganau, Abdullahi Muhammad, ya bayyana cewa, a ranar Talata mutum bakwai sun mutu, inda aka danganta mutuwar da shan shayin.
A cewarsa, ba mu san yawan adadin wadanda suka mutu ba, amma da safiyar Talatar an tabbatar da mutuwar mutane bakwai, inda ya ce, wasun ma ba wanda ya gayyace su zuwa daurin auren sun zo ne kawai don su fake da daurin, don su sha kayan maye.
Ba a dai iya jin ta bakin angon ba, don jin ta nasa bangaren kan lamarin.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa, rundunar da kuma caji ofis na yankin da lamarin ya auku, ba su samu rahoton faruwar lamarin ba.
Amma ya yi alkwarin yin karin haske da zarar ya samu rahoton faruwar lamarin.