Akalla mutane goma ne aka tabbatar da mutuwarsu, da suka hada da dalibai da malamai, sakamakon wani mummunan harbe-harbe da aka yi a wata makarantar sakandire a garin Graz na kasar Austriya.
Hukumomin kasar sun ce wanda ake zargi da kai harin, mutum daya ne kuma shi ma ya harbe kansa da kansa.
- Sarki Sanusi II Ya Yi Hawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda Na Haramta Hawan Sallah A Kano
- Ƙungiyar G-5 Ta Ceto Nijeriya Daga Faɗa Wa Rikici — Wike
Har yanzu ba a bayyana sunan wanda ake zargin ba, har sai an gudanar da bincike da kuma sanar da danginsa.
Masu bayar da agajin gaggawa sun isa wurin jim kadan bayan karfe 9 na safe, inda hargitsi da firgici ya da baibaye mazauna harabar makarantar.
A cewar ‘yansandan yankin, dan bindigar ya shiga ajin karatun ne dauke da bindiga inda ya bude wuta kan mai uwa da wabi, sannan kuma ya harbe kansa.