Mutane biyu ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu hudu suka samu raunuka daban-daban a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Kachia zuwa Kaduna.
Hatsarin wanda ya hada da mota kirar Hilux da Sienna, duk sun yi kaca-kaca sakamakon hatsarin, kamar yadda daya daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu, Mista Simon Salas ya bayyana.
- Tsarin Fallasa Barayin Gwamnati Ya Dusashe — Gwamnati
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Zai Yi Jawabi A Yayin Bude Taro Zagaye Na 2 Na Yarjejeniyar COP15
A cewarsa, “Na hau Hilux daga Kaduna zuwa Kachia, amma a lokaci guda na ce direban ya sauke ni saboda mun gargade shi kan gudun ganganci amma shawararmu.
“Ana haka ne lokacin da ya kawai muka fada wani rami, nan take ya rasa yadda zai yi ya kutsa kai cikin wata mota kirar Hilux da ke tafe,” in ji shi.
An kai mutanen da suka rasu dakin ajiye gawa, yayin da wadanda suka jikkata ke karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Kaduna, bai amsa kiran waya da muka masa ba don jin ta bakinsa kan faruwar hatsarin.