Rundunar ’Yansandan Jihar Borno, ta kama wasu mutane biyu bisa zargin satar adaidaita sahu a unguwar Jajeri da ke Maiduguri.
Kakakin rundunar, ASP Nahum Daso, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 4 ga watan Agusta, 2025, lokacin da wani Abubakar Tijani ya kai rahoton cewa an sace mass adaidaita sahu.
- Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Ƙarin Kasafin Naira Biliyan 215.3 A Na 2025
- Shugaban Zimbabwe Ya Sauka Beijing Domin Halartar Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan
Bayan rahoton, rundunar Crack Squad ta kama wasu mutum biyu; Yakubu Musa da Adamu Musa, dukkaninsu daga Jajeri.
Lokacin gudanar da bincike, sun amsa laifin, kuma an samo adaidaita sahun a wajensu.
Kwamishinan ’Yansandan jihar, Naziru Abdulmajid, ya yaba wa jami’an bisa jajircewarsu tare da tabbatar wa jama’a cewa ’yansanda za su ci gaba da yaƙi da laifuka a jihar.
Ya kuma roƙi jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai don taimakawa wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp