Sama da mutane 20 ne suka kone kurmus bayan wata Tankar dakon man Fetur ta fadi Gadar Rafin Maboro da ke a yankin Ankpa, cikin karamar hukumar Ankpa a jihar Kogi.
Wani ganau ya ce, ibtila’in ya auku ne da misalin karfe 3 a jiya Laraba. Irin wannan ibtila’in shine na biyu a wannan yankin duk acikin wannan Watan.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta jihar (FRSC) Stephen Dawulung, ya tabbatar da afkuwar lamarin, sai dai ya bayyana cewa, har yanzu hukumar ba ta iya tantance adadin wadanda suka mutu ba.
Y a ce, mun tura jami’anmu gurin da lamarin ya auku don su tattara gawarwakin wadanda suka rasun, amma har yanzu, ba mu samu hakikanin adadin wadandda suka mutu a hadarin ba.
Stephen ya bayyana cewa, Tankar da wata mota kirar Bas da kuma wasu Babura uku ne hadarin ya rutsa da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp