Haɗurran hanya da mace-mace suna ci gaba da faruwa cikin ƙaruwa tsakanin shekarun 2024 da 2025, ya nuna an samu ƙaruwar lamarin da kashi 3.9 na haɗura yayin da an samu ƙaruwar mace mace da kashi da 2.2.
Binciken da Jaridar LEADERSHIP ta yi, ya nuna: Alƙalumman da aka samu daga hukumar hana haɗurra ta ƙasa sun nuna cewa cikin watanni shida na shekarar 2025 lamarin ko abin ya nuna abubuwa masu ɗaure kai, saboda kuwa tsakanin watannin Janairu da Yuni, an samu aukuwar haɗurra 5,281 a faɗin tarayyar Nijeriya abinda ya shafi mutane 39,793.
- FRSC Ta Fara Binciken Hatsarin Motar Da Ya Yi Ajalin ’Yan Wasan Kano 22
- Mutane 12 Sun Mutu, 28 Sun Jikkata A Wani Hatsarin Mota A Hanyar Zaria Zuwa Kano – FRSC
Ƙididdigar haknan ma ta nuna mutane 2,838 sun mutu yayin da kuma an samu ceto 17,818, hakan shi yake nuna an samu ƙaruwar haɗurran da kashi 2.2.
Hakanan ma mutanen da suka haɗu da haɗurran sun ƙaru a haɗurran kan hanya,a cikin shi binciken da ka yi da kashi 8.9, idan za’a haɗa da abinda ake da shi a shekar 2024.
A farkon shekarar 2024, daga shikin fasinjoji 36,554 da suka haɗu da haɗurran mota 4,997 tsakanin watannin Janairu zuwa Yuni,sai dai kuma fasinjoji 16,309 sun samu raunuka 2,776 kuma sun mutu.
Alal misali, a watan Janairu 2024, an samu haɗurra gaba ɗaya 990, an samu ceto, 3195, waɗanda kuma suka mutu, 530, mutanen da haɗurran suka rutsa da su7335.
Yayin da yake ƙarin haske akan lamarin Shugaban hukumar, Shehu Mohammed, ya danganta abubuwan da suke faruwa na ƙaruwar haɗurran akan yadda motoci suke ƙaruwa a shekarr 2025.
“Haka abin yake kamar yadda ƙididdigar ta nuna duk a cikin wata shidan, jami’an na FRSC, sun kama mutane 290,887 waɗanda suka aikata laifuka 319,798. Sai dai kuma an kama 250,720 da suka aikata laifi da kuma 271, waɗanda suka saɓawa dokokin Hukumar 2024.Wannan ya nunaan samu ƙaruwar kashi 16 na waɗanda aka kama ko kuma kashi 14.9 na ƙaruwar masu aikata laifuka.
Ƙaruwar da aka samu ta kashi na waɗanda aka, kama sanadiyar aikata laifi bai nuna, Hukumar kiyaye haɗurra, tamkar wata hukuma ce ta, ƙarshen mako.Saɓanin abinda ake tsammani sai ya nuna maganar gaskiya bama kamar yadda ake tsammani ba, tana yin aikin tane kamar yadda doka ta shimfiɗa mata,domin tabbatar da akwai lafiya kan hanyoyinmu ta hanyar takurawar da ba wata abu bace.
“Bugu da ƙari, duk dai a cikin lokacin, fiye da fasinjoji milyan 30 suka yi zurga- zurga inda suka yi amfani da motoci milyan 2.3 a faɗin tarayyar Nijeriya.Yawan motoci da fasinjoji kan hanya yana da matuƙar muhimmanci ta ɓangaren yawan waɗanda suka aikata laifi, aka kuma kama su.
Hakanan ma,an yi kira da mutane domin su taimaka ma irin ƙoƙarin da su ma’ikatan suke yi na tabbatar da cewa hanya ta yi kyau ga muatne matafiya alal misali, Jihohin Anambra da Kano su kaɗai sun samar da mutane fiye da milyan 6.5 na fasinjojin da suke tafiye- tafiye,wanda kuma shi ne kashi 22 na gaba ɗayan fasinjojin da suke tafiya. Waɗannan alƙalumma a fili sun nuna irin yadda ake yawan amfani da hanyoyin, abin yayi matuƙar yawa,domin ya nuna ana damun hanyoyin da kuma su ma’aikatan.’
Da yake bayani kan tsare- tsaren da kuma abubuwan da ake yi,waɗanda za su taimaka wajen rage aukuwar irin haɗurarran da suke faruwa kan hanya, sia Shugaban hukumar ya ce, “Maganar ƙaddamar da yadda bada rahoton labarin aukuwar haɗari (NACRIS) da kuma wata na’urar sadarwa ta zamani ta ( FRSC Mobile App)domin da ita ake yin amfani wajen anfani da hanyoyin da suke tafiyar da ayyukansu.Su waɗancan fasihohi kafar sadarwa ta zamani sun taimaka ƙwarai wajen bada ƙiyasinko ƙididdigar rahoton haɗari,da kuma inganta yadda al’umma suke kasancewa cikin lamarin.
Bugu da ƙari kuma ita na’urar tana bada takamaiman lokacin samar, da bayanai kamar yadda haɗarin ya auku da kuma wurin, bada rahoton gaggawa,Lasisin tuƙi na Direbobi’yadda za’a gano nambar motar da tayi haɗarin, tare da yadda za’a samu hanyar kama Rediyo mai alaƙa da cunkoson motoci a ko ina yake a faɗin duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp