Ministan harkokin cikin gida na kasar Sudan Khalil Pasha Sairin ya bayyana jiya cewa, kimanin mutum 68 ne suka mutu sakamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa da ta afkawa wasu sassan Sudan tun daga wata Yuni.
Sanarwar da ministan ya fitar ta ce, adadin mutanen da suka mutu sakamakon mabambantan dalilai na ambaliyar ruwa da ruwan sama cikin har da rushewar gidaje da nutsewa ya kai 68, yayin da mutum 130 suka samu raunuka.
Fiye da gidaje 4,000 ne suka ruguje gaba daya, kuma gidaje 8,000 sun dan rushe, sannan wasu gine-gine 40 na gwamnati da masu zaman kansu sun lalace, yayin da kimanin murabba’in kilomita 832 na filayen noma suka lalace, kuma wasu dabbobi suka mutu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp