Rundunar ‘yan sandan Jihar Ondo ta ce ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da jefe wani direba mai shekaru 35 har lahira a ranar 10 ga watan Afrilu.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa direban, Olorunfemi Tope ya yi hatsarin da ya yi sanadin mutuwar mutum daya tare da raunata wasu a hanyar Ijoka a Akure.
- Kasar Sin Ta Soki Amurka Bisa Kakabawa Wasu Kamfanoninta Takunkumi Dangane Da Batun Maganin Fentanyl
- Karsashina Yana Ga Rubutun Littafi Ba Fim Ba -Humaira K. Azare
Daga baya direban ya mutu inda aka yada bidiyon lamarin a yanar gizo.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Olufunmilayo Odunlami-Omisanya, ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin a Akure cewa, an kama mutanen bakwai ne da hannu a lamarin.
A cewar Odunlami-Omisanya, daga cikin mutane bakwai, Amos Victor, Boboye Ismail, Olatunji Samuel da Farotimi Pelumi, su ne manyan wadanda ake zargin.
Ya ce suna cikin wadanda aka dauka a faifan bidiyon suna kai wa marigayin hari.
Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bisa zarginsu da kone-kone da kuma kisan kai, bayan kammala bincike.
“Mun sha fada ba adadi cewa ya sabawa doka daukar doka a hannu.
“Lokacin da wani hatsari ya faru, abin da muka fi mayar da hankali a kai shi ne yadda za mu kubutar da wadanda abin ya shafa ta hanyar kai su asibitoci mafi kusa don ba da agajin gaggawa ba tare da daukar doka a hannunmu ba.
“Ba daidai ba ne kowa ya dauki ran kowa ba; ya kamata mu bar doka ta dauki matakinta,” in ji kakakin.