Jami’an rundunar ‘yansandan Jihar Gombe sun kama wasu mutum biyu Ibrahim Umar mai shekaru 22 da Usman Abdullahi mai shekaru 27 bisa zarginsu da hada baki da fasa gidaje da kuma sata.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan, DSP Buhari Abdullahi, an kama wadanda ake
- ‘Yansanda Sun Kubutar Da Wata Mata Da Aka Yi Garkuwa Da Ita A Otal Din Abuja
- ‘Yansanda Sun Cafke Wani Ɗalibi Da Ya Kashe Abokinshi Da Gatari A Nasarawa
zargin ne biyo bayan wani bincike da aka gudanar kan wani korafi da aka samu a ranar 4 ga Fabrairu, 2025.
Koken da Abdulbasid Haruna ya shigar, ya yi zargin cewa wasu da ba a san ko su wanene ba suka shiga gidansa a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, da misalin karfe 1:00 na dare, inda suka yi awon gaba da kayayyaki da dama da suka hada da Laptop, wayoyin hannu, da wasu kayayyaki masu daraja wadanda adadinsu ya kai Naira miliyan 3,200,570.
Ya ce, “Mun yi amfani da fasahar kere-kere tare da gano wasu na’urorin da aka sace, wanda hakan ya sa muka kama wadanda ake zargin.
“A binciken da ake yi, an gano dukkan kayayyakin da aka sace bayan an sayar da su kan kudi naira 80,000, kuma wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata laifin.”
PPRO ya kara da cewa, ‘yansanda na ci gaba da neman mutum na uku da ake zargi mai suna Ibrahim Danmariya, wanda ake kyautata zaton shi ne mai karbar kayan da aka sace. Abdullahi ya bukaci mazauna yankin da su lura kuma su kai rahoto ga ofishin ‘yansanda mafi kusa.
“Muna kira ga jama’a da su bayar da bayanai masu amfani da za su kai ga kama wanda ake zargi da gudu.
“Muna tabbatar wa jama’a cewa za a yi amfani da duk bayanan cikin sirri,” in ji Abdullahi.