Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da harkokin jin kai, (UNOCHA) ya ce, kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 7.9 ne suke cikin halin neman taimakon gaggawa da na jin kai a jihohin Borno, Adamawa da kuma Yobe.
Jihohi uku sun sha fama da matsalolin rashin tsaro, musamman na Boko Haram, wanda ya janyo hallaka dubban mutane da tursasa wa wasu miliyoyi yin gudun hijira na dole tsawon shekaru kusan ashirin.
- An Ceto Ɗalibai 20 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Binuwe
- Hukumar Haraji Ta Nemi A Samar Da Dokar Sa Ido A Kan ‘Yan Kirifto
A yayin bikin tunawa da ranar jin kai ta duniya na wannan shekarar da ya gudana a ranar Litinin a Yola, UNOCHA da take baje kolin kiddigar ta nuna cewa adadin mutum miliyan 3.9 ne suke neman tallafi a Jihar Borno, yayin da Jihar Adamawa ke da adadin mutum miliyan 2.2, inda ita kuma Jihar Yobe ke da adadin mutum miliyan 1.8 ke tsananin bukatar agajin gaggawa.
Kiddigar ta kuma nuna cewa mata da yara sun kunshi kaso 80 cikin 100 na wannan adadin masu neman abinci mai gina jiki.
Ko-odinatan shirin a Nijeriya, Mohamed Malick Fall, ya nanata matsalar karancin abincin mai gina jiki a shiyyar, kaso uku ne kawai na cikin dala miliyan 306 da aka bukata domin magance matsalar ne aka samu zuwa yanzu.
“Dole mu hada karfi da karfe mu yi aikin jin kai domin dakile wahalar da suke sha,” Fall ya bukata.
A Jihar Adamawa lamuran sun kara tabarbarewa ne sakamakon kwararowar ‘yan gudun hijira 33,000 daga kasar Kamaru, wadanda suka tsere wa hare-haren kungiyoyin ‘yan bindiga, a cewar hukumar samar da agajin gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA).
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, da ya samu wakilcin mataimakinsa, Farfesa Kaletapwa Farauta, ya jaddada muhimmancin hada karfi da karfi domin tunkarar matsalar.
Ya ce dole ne a ci gaba da aikata kyawawan abubuwan da za su kasance na jin kai da tausayin wadanda suke cikin halin bukatar hakan domin kyautata rayuwa a kowani lokaci.
Shugaban Ofishin Majalisar Dinkin Duniyan da ke Damaturu, Dabid Lubari Lominyo shi ne ya sanar da wannan yayin da ke ganawa da ‘yan jarida kan ranar jin kai ta duniya. Bayanan sun fito ne daga rahoton ofishin sakatare janar na majalisar dinkin duniya na 2024 kan kare fafaren hula daga rikice-rikicen ta’addanci.
Lominyo ya bayyana cewar kare hakkin fafaren hula shi ne babban abun da suka sanya a gaba domin karesu daga hare-haren ‘yan bindiga masu aikata ta’addanci. Ya lura kan cewa hare-haren Boko Haram ya tuguza tattalin arziki sosai.
Ya roki dukkanin masu hannu da masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro da su kara himma da azama wajen ganin rayukan fafaren hula sun samu kariya da kiyayewa a kowani lokaci.