Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Usman Ododo, ya bayyana matukar alhininsa kan rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma dattijon kasa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, inda ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga Nijeriya.
A sakon ta’aziyyar da ya fitar a madadin gwamnati da al’ummar jihar Kogi, kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya ce marigayi Dantata “ba wai dan kasuwa ne kawai ba da ya yi , wata cibiya ce da sunanta kadai ke nuni da gaskiya, karamci, da sadaukarwar ci gaban kasa.”
Sanarwar ta ce Gwamna Ododo ya samu labarin rasuwar Dantata da bugawar zucciya, sannan ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan Dantata, gwamnati da al’ummar jihar Kano da ‘yan kasuwa da ma kasa baki daya.














