An ɗage wasanni huɗu na gasar Serie A ta ƙasar Italiya da aka shirya yi a ranar Litinin bayan mutuwar Paparoma Francis, Fadar Vatican ta sanar a safiyar yau litinin cewa Paparoma Francis ya mutu yana da shekaru 88, bayan an sallame shi daga asibiti kwanan nan bayan shafe makonni biyar ya na jinya.
Wasanni hudu na Seria A da su ka hada da Torino Vs Udinese, Cagliari Vs Fiorentina, Genoa Vs Lazio da kuma Parma Vs Juventus duka an soke yinsu bayan da aka shirya buga su a ranar Ista wato yau Litinin, wanda ya zama ranar hutu a kasar Italiya.
- An Yi Bikin Murnar Cika Shekaru 20 Da Kafa Cikakkiyar Dangantakar Abokantaka Bisa Manyan Tsare-tsare Tsakanin Sin Da Italiya A Milan
- Shugabannin Sin Da Italiya Sun Kalli Kayayyakin Tarihi Da Aka Dawo Da Su Kasar Sin
A maimakon haka za a buga wasannin a ranar Laraba, 23 ga watan Afrilu, an zabi Paparoma Francis ya jagoranci cocin Katolika a shekara ta 2013, inda ya maye gurbin Paparoma Benedict na 16, Paparoma wanda ya mutu yanada shekaru 88 ya kasance sanannen mai sha’awar kwallon kafa kuma yana goyon bayan kungiyar San Lorenzo ta Argentina tun yana yaro.
Mabiya addinin kirista a fadin Duniya musamman Turai da wasu kasashen Afirika sun yi makokin mutuwar Paparoma, inda suka bayyana shi a matsayin mutum mai taka tsan tsan da son zaman lafiya, wanda kuma sukace rashinsa wani babban gibi ne da zai yi wuyar cikewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp