Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya tabbatar da mubaya’arsa ga Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023.
BBC ta rawaito cewa, har yanzu dai Wike ya ce yana nan a kan bakarsa cewar dole shugaban jam’iyyar ta Peoples Democratic Party Iyorchia Ayu ya sauka daga muƙaminsa.
- Kwamitin Amintattu Na PDP Ya Gana Da Wike Kan Rikicin Jam’iyyar
- 2023: Atiku Ya Karyata Batun Zai Goyi Bayan Wike A Zaben 2027
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Wike ya tabbatar da haka ne a wani taro da ya yi da ‘ƴan takarar jam’iyyar na jihar Rivers a mataki daban-daban, a garin Port Harcourt, a daren Alhamis.
Wike ya ce ana iyakar bakin ƙoƙari wajen ganin an warware rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar sai dai wasu ƴan-ba-ni na-iya ne suke kawo cikas.
Ya ce “An gama zaɓen fitar da gwani. Na ce a cire ɗan takarar shugaban ƙasa ne?
Ko na ce a cire ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa? To mene ne kuma ake ba ni haƙuri a kai?
“Abin da nake cewa shi ne tunda kun samu ɗan takarar shugaban ƙasa to ku ba mu muƙamin shugaban jam’iyya.”