Daya daga cikin Jaruman fina-finan Hausa cikin masana’antar Kannywood Amina Haruna Abdullahi wadda aka fi sani da Amina Miloniya, ta fyede biri har wutsiya dangane da yadda ake gudanar da daukar shirin fim, da kuma yadda rayuwar ‘yan fim din ke kasancewa. Bugu da kari Jarumar ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta, tare da irin matakan da ta bi wajen samun nasarar shiga cikin masana’antar. Haka zalika Jarumar ta bayyanawa masu karatu gaskiyar al’amari game da batun da ke zagawa a gari na rashin zaman aure ko kin yin aure ga Jarumai mata, har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SIDI BALA Kamar haka;
Masu karatu za su so su ji cikakken sunanki tare da dan takaitaccen tarihinki
Sunana Amina Haruna Abdullahi, wacca aka fi sani da Amina Maloniya. Ni haifaffiyar garin Jos ce, na yi makarantar firamare da sakandare duk a garin Jos, yayin da na shiga J.S.S 3 aka yi min aure ba tare da na karasa ba. Daga baya na kuma auren ya mutu.
Bayan da kika fito daga gidan mijin, shin kin ci gaba da karatun ne ko kuwa iya karatunki na baya ki ka tsaya?
Gaskiya ban ci gaba ba a iya nan na tsaya, na tsaya iya J.S.S 3. Bayan na yi aure na haifi yara 3, daga baya kuma Allah ya kawo rabuwa tsakaninmu muka rabu, ban ci gaba ba, amma ina da buri nan gaba in sha Allah.
Waccee rawa kike takawa cikin Masana’antar Kannywood?
Ina taka rawar Jaruma, matsayin uwa.
Me ya ja hankalinki har kika tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Eh! Gaskiya abin da ya ja hankali na har na shiga masana’antar Kannywood abu daya ne zuwa biyu; Tun ina budurwa gaskiya ina da wannan ra’ayin, to kuma daga baya na zo na yi aure, aurena ya mutu sai na ga bari na yi amfani da wannan damar na samu na shiga ciki tun da ina da niyya ina da ra’ayi. Toh! akwai wani guri da ake rihazal a wata Islamiyya Asabar da Lahadi, ina dan zuwa kallo sai nake tambayarsu idan ina so na shiga ya zan yi ko ya ake yi?, sai suka ce mun zan sayi ‘fom’ da farko, bayan na sayi fom zan zo da magabatana kamar wan baba, ko kanin baba, ko ‘Wa’ don su tabbatar da cewar da saninsu na shiga harkar, kuma suna so na da shi. Toh! sai na je da wana ya karbar min ‘fom’ din ya cike, sannan na dan fara zuwa rihazal har na zo na shiga cikin masana’antar.
Idan na fahimce ki kina so ki ce baki sha wata wahala ba wajen shiga masana’antar, ko ya abin yake?
Tab! di jan, na sha wahala sosai gaskiya, saboda kin san irin wannan ba abu ne da za a ce kana so da wuri kuma ka cimma bukatarka da wuri ba, na fada miki tun a farko tun ina budurwa nake da ra’ayin yin hakan, toh bayan na shiga kin san dole mutum zai samu matsaloli kala-kala. Za a ce za a tafi wajen daukar shiri ka kama hanya ka je, haka za ka je ka wuni ka dawo ko ‘workers fast’ ba a saka ka ba, kawai dai aikin yana bukatar hakuri da juriya, amma ba wanda zai ce ya shiga ba tare da ya sha wahala ba amma ban san wasu ba, gaskiya mu dai kam Jos ba sauki har ga Allah.
Ba kya ganin mutane za su iya cewa kamar son da kike yi wa harkar fim ne ya sa har kika yi kokarin fitowa daga gidanki?
To kin san dan’Adam ba a iya masa, kowa da irin abin da zai ce, baka isa ka hana dan’Adam fadar ra’ayinsa ko abin da ya yi niyya ba. Kwata-kwata mutuwar aure na ba shida jibi ko alaka da maganar fim don kaddara kawai ta riga ta fata ba yadda za a yi, don ina tunanin kafin na fara sai da na kai shekara daya da mutuwar auren na zo shiga masana’antar, amma ban san ko ana fada ko a bayan idona ban ji ba, amma gaskiya a gaban idona ban taba samun irin wannan matsalar ba. Saboda ba wai daga mutuwar aurena fara fim ba, a kalla na kai kamar shekara daya kafin na zo na fara.
Za ki kamar shekara nawa da fara fim?
Zan kai kamar shekara daya da rabi gaskiya.
Da wanne fim kika fara?
Na fara da fim din ‘Jejin Sunkuru’, daga baya na zo nabyi ‘Kasar Ajali’, akwai su dai da yawa gaskiya, wadanda sunayensu ma ba lallai na iya lissafa miki yanzun nan ba.
Ya batun iyaye lokacin da ki ka fara sanar musu cewar; kina son shiga cikin masana’antar, shin kin fuskanci wani kalubale daga gare su ko kuwa?
Eh! to, a gaskiya ban samu wani kalubale ba, mahaifina Allah ya yi masa rasuwa, sai mahaifiyata ta rage ban samu matsala da ita ba. Amma na samu matsala da kanin mamana, don akwai lokacin da ya taba zuwa gida wajen ziyarar mamana, sai ya ke tambayarta ina nake, sai ta ce mishi ai na tafi fim, sai ya ce mata “fim kuma, wanne irin fim, a ce kina raye kuma ki bar Amina ta rika fim, gaskiya bai dace ba.” Bayan nan sai ya dawo gida washegari ya yi min fada cewar kar na kara zuwa me zai kai ni wani fim da sauransu, to daga baya gaskiya sai na je na samu irin yayyensa da sauransu duk aka hadu dai aka bashi hakuri, tun daga ranar dai bai kara dawowa ya yi min magana ba, har yanzu, shi ne dai na ci gaba da yi kawai.
Toh ya batun kan ta waye da ake yi wa wasu idan za su shiga cikin masana’antar, shin ke ma kin taba fuskantar hakan ko kuwa?
Gaskiya tsakani da Allah ni ban ci karo da irin wannan ba, saboda ina ji ma dai mata da dama ana kan ta kile da sauransu, gaskiya ni ban samu wannan matsalar ba, ko don mu ba yara bane shi ya sa ban samu wannan matsalar ba, asali ma ni ban san ni ya ake yin wannan kan ta kile ko kan ta waye ne. Abu daya na sani a da ana cewa kawo kudi zan hada ki da Darakta wane zai yi aiki da ke, shi ma dai kan ta waye ake cewa, ki ba da wani abu zan hada ki da wane da dai sauransu, wannan dai zan ce na samu irin wannan matsalolin a baya. Amma gaskuya ni kam ban hadu da irin wancen da ake fada, ban samu ba.
Ya farkon fara dora miki kyamara ya kasance?
Gaskiya na samu matsaloli sosai, dan farko na kai kamar wata uku ina zuwa rihazal ba a taba samun kyamara ba, to farkon da aka fara samun kyamara shi ne; fim din Jejin Sunkuru idan na yi a ce bai yi daidai ba na sake, haka zan yi a ce sake a haka dai, gashi kuma yanzu Allah ya sa ka iya kuma har kai kake gyarawa wasu.
Wanne fim ne ya zamo bakandamiyarki cikin fina-finan da kika fito?
Gasar Ajali, sai wakar Labarina da muka yi.
Wanne fim ne ya taba baki wahala, kuma a wanne waje ne ki ka sha wahala?
Fim din da ya bani wahala shi ne Kasar Ajali, akwai yarinya na a fim din da aka yi wa fyade har ta kai ga an zo asibiti, a wannan gurin gaskiya na sha wahala kafin na rike ‘dialogue’ dina da dai sauransu.
Bayan kalubalen da kika fada a baya, ko akwai wani kalubale da kike fuskanta a yanzu cikin masana’antar?
Wallahi yanzu kam! ba ni da wata matsala da nake fuskanta, matsala daya ita ce; irin mutum ba shi da lokacin kansa, yana dan zama za a kira shi ya zo aiki da sauransu, shi kuma daman wannan don haka ka shiga, ban dauke shi matsala ba.
Wanne irin nasarori ki ka samu game da fim, ko ana kan samu?
Eh! Na samu da dama ma, amma dai sirri ne.
Ya kika dauki fim a wajenki?
Gaskiya na dauki fim sana’a, a haka kawai na dauke shi.
Me kike son cimma game da fim?
Abin da nake son na cimma shi ne; zuwa nan da dan lokaci kadan in Allah ya fito mun da miji na yi aure, gaskiya yanzu babban abin da nake son na cimma kenan Alah ya fito mun da miji nagari na samu na yi aure.
Wace rawa ki ka fi son takawa a cikin fim?
Ina son na fito masifa, irin na fito a masifaffiya wannan wajen yana mun dadi, ina son wajen.
Zamu ci gaba a mako ma zuwa