Shafin da ke zakulo muku fitattun Jarumai da mawaka manya da knana dake cikin masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannywood, har ma da wadanda suka yi fuce, Shafin yau na tafe da daya daga cikin masu shirya fina-finan Hausa kuma Jarumi me taka rawa a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood wato MUDASSIR ISYAKU D.T.M, Jarumin da ke taka rawa cikin fina-finan da ke haskawa a yanzu, Jarumin ya bayyana babban kalubalen daya fuskanta bayan shigarsa cikin masana’antar Kannywood, baya ga haka Jarumin yayi karin haske ga masu kallo da masoyansu, dangane da irin rashin lokutan da sauran Jarumai ke rasawa yayin da suke bukatarsu, tare da kira ga gwamnati wajen magance matsalolin da ke afkuwa a cikin masana’antar, har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Masu kartu za su so su ji cakakken sunanka.
Sunana Mudassir Isyaku D.T.M ma’anar D.T.M ‘Dutsan-ma Katsinma state channel’ garin iyayena, amma ni an haife ni a Jihar Kano Rijiyar Lemo.
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
Tarihina shi ne; Na yi ‘Primary school’ a Rijiyar lemo ‘Sulaiman Chamber’, nayi ‘Secondary School, Warure Gwale Local Gobernment’, a yanzun haka ana ci gaba da yi. Ba ni da aure, aure sai nan gaba in na samu wadda take sona.
Wanne mataki ka tsaya a karatunka, kuma bayan karatu kana aiki ne ko iya karatun kake yi?
Ina matakin N.C.E, kuma ina aiki, ni Furodusa ne kuma Jarumi a masa’antar Kannywood.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Tun ina karami nake son harkar fim, don bana mantawa a kafa nake zuwa Mandawari Sabon Titi ofis din ‘DIRECTOR ISHAK SIDI ISHAK’ ba don komai ba sai don in ga ‘yan fim.
Za ka yi kamar shekara nawa cikin masana’antar Kannywood?
Zan kai shekara 6, da fara ‘acting’ kuma shekara 2.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
An sha wuya shiyasa yanzun Alhamdulillah, don daga gida za ka fara fuskantar kalubale.
Wanne irin kalubale ka fuskanta daga wajen iyayenka lokacin da ka fara sanar musu kana son shiga cikin masana’antar?
Wurin mahaifina na samu dama, wurin ‘yan uwa kuma dangin mahaifina sune suka runka bani matsala tun daga Katsina aka zo aka gayawa mahaifina an ganni a fim, amsar daya bayar ita ta bani dama, sakamakon ni yadda nake tunani ba zai bar ni in yi fim ba, don haka ni ban gaya masa ba kuma zan je ‘location’, amma ba zan fito a inda za a ganni ba, sai wurin taron jama’a. Sai muka je wani fim BABAN SADIK na Nafisa da Adamu na fito a kotu.
Ya farkon fara shirya fina-finanka ya kasance, musamman yadda za ka ji wasu na kukan samun faduwa a farkon farawarsu, shin kai ya abin ya kasance ko kwalliya ta biya kudin sabulu?
Haka ne, amma gaskiya ni na san komai, in baki manta ba na gaya miki cewa na dade, kawai dai ni ba zan yi ba, har sai da amincewar mahaifina, kuma dama shi fim mataki ne akwai nasarori da dama a ciki.
Wanne fim ka fara shiryawa, kuma za su kai kamar guda nawa?
BANI DA LAIFI da WATA RANA, kusan a tare na yi su, za su kai kamar guda biyar.
A wanne fim ka fara fitowa, kuma wacce rawa ka taka cikin fim din?
Fim djn dana fara fitowa WATA RANA.
Ya ka ji a lokacin da za ka fara fitowa a fim matsayin jarumi ba mashiryin shirin fim ba?
Ana gobe za a fara ‘Shooting’ kasa bacci na yi, saboda murna, wurin gabatar da fim din kuma aka hada ni da TAHEER FAGGE da LADIDI FAGGE sai suka bani kwarin gwiwa.
Bayan shigarka masana’abtar Kannywood ko akwai wani kalubale da ka ci karo da shi cikin masana’antar?
Kwarai kuwa, kalubalen dana fuskanta wanda ba zan taba mantawa da shi ba a cikin masana’antar Kannywood shi ne; Akwai wata rana da wani bawan Allah ya kira ni, ya ke ce mun ya tsinci wata waya na zo na karba, kuma aka ci sa’a a unguwarmu ne a tsallake, da na ne sai na na yi mamaki wai ya ga lambata a ciki. haka na yi ta bin shi na ce “kai! ni ban san wannan number ba”, a karshe dau na gano wani ma’aikacin ‘Police’ a ‘wani dibision anan unguwarmu. Kin san yanayin fim idan kana yi za ka gane wani abun, Na gano shi sa’in daya fara magana, yanayin yadda ya ke magana ko ’emotion” dinsa za ka yi ‘understanding’. Sai na ce masa “ka ga bawan Allah a ina kake?”, ya ce shi dan sanda ne, a ina? ya fadan sai na ce masa ‘me ya ke faruwa yi mun bayani?”, shi ne ya ke bani labarin zargin da ke tsaninsa da matarsa, Ta fita ta tafi ba a san inda ta tafi ba, duk garinsu Katsina gidan iyayenta da ko ina amma ba a ganta ba, duk gidan ‘Yan uwanta na Kano da Katsina ba a ganta ba, sai da tayi kwana goma, sannan ta dawo. Tana dawowa sai ya kwace wayarta, yana karbar wayar sai yayi ‘Searching’ din lamba sai ya ga lambata kuma an rubuta ‘My’. Toh! sai ya ce mun wayar ta mace ce, sai na ce wace ce ita macen?, sai ya ce ‘wannan macen ai da alamun sunanta Nafisa”, anan na fada masa ina da Nafisa kuma a Katsina take, amma ita uwa ce a wurina, ya ce “eh! ita ma a Katsina take”, na ce a wanne gari? ni a Dutsanma take, ya ce shi kuma a Batagarawa, kin ga mun dan samu kilashin. Sai ya ce mun “A gaskiya….!” na ce “ka ga bawan Allah, wannan dogon turancin da muke fito gaya mun, me ya ke faruwa?”, sai ya ce gaskiya matarsa ce, ya labartan labarin yadda aka yi, ya ce bayan ta dawo ya karbi wayarta yana dubawa ya ga lambata ta sa “My”, na ce toh ni nafisar da nake da ita da ta sa My sai da ta karasa My son. A karshe dai sai na gano ashe irin matan nan ne da za su ga ‘number’ a cikin fim su dauka, wannan ‘case’ din abun ya batan rai, kuma ya tayar mun da hankali, dan akwai kanina ‘Police’ na kira shi, kafin ma wannan lokacin shi police din na kira shi na ce kana ina yanzu?, sai ya ce ya akai? na ce yana ina zan je na same shi, ai maganar aure ba abun wasa bane, na ce ni furodusa ne ina shirya fim, kuma zan iya sa number na a cikin fim ta gani ta dauka, da kansa ya ke cewa ba sai na zo ba, karshe dai washegari sai da na kira wannan kanin nawa muka je har gurin nake masa maganar. Sai ya ke cewa ai shi tun daga maganar da ya ji ina cewa yana ina na zo na same shi? ya ji cewa ba hannuna, sabida in ba ni da gaskiya ba zan nemi inda yake ba, tunda ya fada mun shi ‘Police’ ne. Toh wannan kadan daga cikin irin kalubalen dana fuskanta a cikin fim, wanda ko yaushe bana ita mantawa da shi.
Za mu cigaba a mako mai zuwa