Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Litinin, ya bayyana cewa shekaru bakwai da ya yi a kan karagar mulki a matsayin “masu wuya”, inda ya ce ya “ya matsu ya sauka”.
Rahotanni sun rawaito cewa a wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya sanya wa hannu, shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu gwamnonin jam’iyyar APC, ‘yan majalisa da shugabannin siyasa a gidansa da ke Daura, a jihar Katsina.
- Daura Zan Koma Da Zama Idan Wa’adin Mulkina Ya Kare – Buhari
- Buhari Ya Roki ASUU Kan Sake Duba Matsayarsu Ta Yajin Aiki
Ya ce, “Sarkin Daura, Dakta Faruk Umar, a filin idi ya gano cewa na yi watsi da tushe na. Ya rike lasifika ya na shaida wa kowa cewa tun 2021 rabon da na yi bikin sallah.
“Nan da watanni 10 zuwa 11, zan dawo nan. Ina da gida mafi kyau a Kaduna, amma ba zan zauna ba saboda kusancinsa da Abuja.”
“Na kagu na sauka da ga mulki. Zan iya gaya muku cewa gaskiya da wahala. Ina godiya ga Allah da mutane suka yaba sadaukarwar da muke yi. Ina yi wa wanda zai gaje ni fatan alheri,” inji shi.