Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce, ya nuna iya gaskiyarsa a jagorantar Jihar a lokacin shugabancinsa.
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a wani martani ga rahoton da ya bada shawarar a bincike shi.
- Kwamitin Majalisar Kaduna Ya Bayar Da Shawarar A Binciki El-Rufai
- Gwamna Dauda Lawal Ya Jaddada Ƙudirinsa Na Tsaron Rayukan Al’ummar Zamfara
in ba a manta ba, mun rahoto muku yadda kwamitin wucin gadi da aka kafa don binciken gwamnatin El-Rufai ya mika rahotonsa, a ranar Laraba ga Majalisar jihar.
Da yake karbar rahoton, Kakakin Majalisar Dokokin Kaduna, Yusuf Liman, ya ce gwamnatin El-Rufa’i ta karkatar da Naira biliyan 423 a yayin da ta bar jihar da dimbin bashi.
Kwamitin ya ba da shawarar gudanar da bincike tare da gurfanar da El-Rufai da sauran jami’an gwamnatinsa ga hukumomin tsaro da ke yaki da cin hanci da rashawa.
Rahoton ya yi kira da a gaggauta dakatar da kwamishinan kudi na jihar Kaduna, Shizer Badda da shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar.
Amma da yake mayar da martani a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar a madadinsa, El-Rufai ya ce yana alfahari da irin nasarorin da ya samu a bangaren jagoranci.