Dakataccen Kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa (REC), Barista Hudu Ari, ya jaddada matsayarsa kan iƙirarin cewa, Sanata Aisha Binani ta jam’iyyar APC ce ta lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa a zaɓen da aka gudanar a shekarar 2023.
Ari wanda ya rantse da Al-Ƙur’ani yayin da ke kare matsayarsa, ya haƙiƙance kan cewa, shelanta Binani da ya yi a matsayin wacce ta lashe zaɓen ya yi bisa gaskiya da kwararan hujjoji.
- ‘Yansanda Sun Cafke Wani Ɗalibi Da Ya Kashe Abokinshi Da Gatari A Nasarawa
- Me Dakatarwar Da Pillars Ta Yi Wa Usman Abdalla Ke Nufi?
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida a gidansa da ke Bauchi a ranar Asabar, 8 ga watan Fabrairu, Barista Hudu Ari ya ce, ya samu shaidun da suke tabbatar da cewa, Binani ta kayar da gwamna mai ci, Ahmadu Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP a yayin zaɓen.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe ba daidai ba, lamarin da har ya kai an gurfanar da shi a kotu.
Ari ya nuna damuwarsa kan yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe suka shafa wa idanunsu toka suka ƙi hango hujjojinsa da ya gabatar na kura-kuran da aka tafka a lokacin zaɓen.
Hudu wanda ya ɗauki Alkur’ani mai girma yayin hirar, ya rantse da Allah cewa, matakin da ya ɗauka a yayin ayyana sakamakon zaɓen ya yi ne da zuciya ɗaya kan gaskiya da kuma bisa dokokin gudanar da zaɓe.
Ari ya kuma ce INEC da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ba su ba shi damar kare kansa da ji daga gareshi ba, kuma shaidunsa da suke nuna cewa, Binani ce ta yi nasara an yi watsi da su ba tare da zurfin tunani ko nazarta ba.
Ya ce, hatta korarsa da shugaban ƙasa ya yi an yi ne kawai domin ɓata masa kima da mutunci.
Kan zargin da aka masa na cewa ya karɓi cin hancin biliyan 2 a wajen ‘yan siyasa domin kare ko yin abun da zai zama alfanu ga Binani, Ari ya ƙaryata. Ya sanar da cewa yanzu haka yana tuntuɓar iyalansa kan ko zai nemi haƙƙi a kotu kan zargi marar tushe da aka masa na amsar na goro, tare da cewa, “Nijeriya ƙasarmu ce dukka, ya rage namu mu kare ƙasar ko mu lalata ta.”
Da ya ke bayani kan zamansa a ofis, ya ce, ya samu nasarar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisu ba tare da wani ce-ce-ku-ce ba.
Ya yi iƙirarin cewa batutuwan da suka taso lokacin zaɓen gwamnan jihar da ‘yan majalisun jiha a rumfunan zaɓe 69 su ne suka janyo rikici da har ya kai ga korarsa.