Jarumar Kannywood Khadija Ahmed wadda akafi sani da Khadija Mai Numfashi a wata hira da ta yi da jaruma Hadiza Gabon a cikin shirinta mai suna Gabon’s Room Talk Show ta bayyana yadda ta sha gwagwarmaya a lokacin da ta nuna sha’awar fara fitowa a cikin shirin fina-finan Hausa na Kannywood.
Jarumar wadda hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano (Kano State Censorship Board) ta dakatar daga shiga duk wata harka ta shirin fim na tsawon lokaci sakamakon wani faifan bidiyo nata da ta dora a kan shafinta na Tik Tok ta bayyana cewar ta sha wahala kafin a amince mata ta shiga masana’antar Kannywood a wancan lokacin.
- Tsohuwar Jarumar Kannywood Fati Slow Ta Rasu
- Rahama Sadau: Daga Jarumar Kannywood Ta Zama Jarumar Bollywood
A lokacin da na bukaci shiga harkar fim sai na tuntubi Ayatullahi wanda a wancan lokacin yake kamar saurayina, sai ya nuna mani cewar ba za a fara haskani a cikin shirin fim ba sai da umarnin iyayena, ni kuma da yake ina matukar sha’awar fitowa a cikin shirin fim a wancan lokacin sai nace masa an amince in fara fim a gidanmu, in ji Mai Numfashi.
Ta ci gaba da cewa bayan na fito a wani fim ne sai kanin mahaifiyata ya kira ni, a lokacin da ya nuna mani bidiyon sai yake tambayata nan wacece kafin in bashi amsa tuni ya falla mani mari a kumatu ni kuma na fashe da kuka.
Haka dai na ci gaba da ganin kalubale kala kala inda gaba daya ‘yan uwan mahaifiyata suka ki amincewa in yi fim har sai lokacin da aka tafi dani da mahaifiyata har inda ake daukar wani shiri, bayan taga yadda ake yi sai ta ce mani indai har iyakar abinda ake yi kenan a fim to ina yi maki fatan alheri Allah ya bada sa a.
Da aka tambayeta a kan ko ta yi nadamar abinda ta aikata har yaka ga hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano a karkashin jagorancin Abba El Mustapha ta dakatar da ita daga shiga duk wata harka ta fim na tsawon wani lokaci.
Sai Khadija ta ce maganar nadama kam sosai ta yi nadamar abinda ta aikata har ya kai ga an dakatar da ita, inda kuma ta ce a halin yanzu ta yi wa kanta fada domin ganin cewar hakan bata sake faruwa anan gaba ba.