Marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya shiga rundunar sojin Nijeriya, shi ne domin gujewa auren fari da wuri da aka so yi masa a ƙuruciyarsa a garinsu na Daura, Jihar Katsina a yau.
Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake hira da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, a gidansa da ke Daura, bayan barinsa mulki a shekarar 2023.
- Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Sanar Da Dakatar Da Ayyukanta Saboda Alhinin Rasuwar Buhari
- Rasuwar Buhari: Gwamnatin Katsina Ta Ayyana Yau Litinin A Matsayin Ranar Hutun Aiki A Jihar
Bidiyon hirar, wanda ya sake bayyana a kafafen sada zumunta bayan rasuwarsa, ya nuna Buhari cikin walwala yana ba da labarin rayuwarsa bayan kammala karatun sakandare.
Pantami ya tunatar da Buhari kan irin nasarorin da ya samu a aikin soja, musamman a Gombe tsakanin 1984 da 1985.
A martaninsa kan dalilin shiga soji, Buhari ya ce: “Na shiga soja ne domin gujewa aure da wuri da aka shirya yi min.”
Ya ƙara da cewa: “Bayan shekaru tara da na yi ina karatu a Katsina, shekara uku a makarantar firamare ta gaba da sakandare shekaru shida, na dawo gida, sai suka shirya yi mini aure. Wata rana na ci karo da wani da ban san shi ba wanda daga baya aka ce ɗan uwan mahaifina ne. Ya buƙaci na kai shi wurin mahaifiyata, kuma daga baya aka ce an ba ni diyarsa ta aureni, ko yana raye, ko bayan ba ransa ya ba ni ɗiyarsa halin.”
Ya ce, a lokacin da ya gama karatu, an yi masa tayin aiki da albashin fam £12.10 da babur da kuma mata damar zama a wurin na har abada.
“A lokacin ne na yanke shawarar na gudu, na shiga aikin soja,” in ji shi cikin dariya. “Mahaifiyata ta damu ƙwarai saboda haka, na ci gaba da bata hakuri har tsawon lokaci. Ta ce tana so ta ga zuriyar ɗanta na ƙarshe. Haka na samu kaina a cikin soji.”
Marigayi Buhari, wanda ya mulki Nijeriya a matsayin shugaban mulkin soja daga 1983 zuwa 1985, sannan kuma ya sake zama shugaban ƙasa a mulkin dimokuraɗiyya daga 2015 zuwa 2023, ya rasu a asibiti da ke Lolandon yana da shekara 82, bayan fama da rashin lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp