Fitaccen malamin Darika a Afrika, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce, dukkanin wani mutumin da ya taba masa wani laifi to ya sha kuruminsa domin kuwa ya yafe wa kowa.
A daidai lokacin da yake yafe wa mutane, shi ma ya roki dukkanin wani da ya masa wani laifi da ya taimaka ya yafe masa domin a cewarsa ya riga ya gama samun biyan bukatu na abubuwan da yake burin samu a wajen Allah illa guda daya.
- NCAA Ta Dakatar Da Max Air Daga Jigilar Fasinjoji A Nijeriya
- Yau Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da Emefiele Ya Shigar
Kodayake ga sauran dayan ma, Sheikh Dahiru Bauchi ya yi fata da rokon Allah cika masa. Ya ce, babban abun alfahari a gareshi yadda ya kyankyashe zakakuran mahahaddata Alkur’ani mai girma da babu adadi.
Daya daga cikin ‘ya’yan malamin, Sayyid Ali Sheikh Dahiru Bauchi shi ne ya shelanta wa duniya wannan yafiyar na mahaifinsa a lokacin da ke jawabi a wajen wani taron karrama daliban da suka kammala karatun Alkur’ani na makarantar Sayyid Ali da suka koyi Kira’a a ranar Alhamis.
Ya ce, “Ina mana albishir na cewa Maulana Sheikh ya ji irin karatun da almajiransa suke yi, ya saurara yana bibiya, ya ji suna karatu da kira’o’i da dama da yawa, ya ce wannan abun ya masa dadi, masa dadi saboda ya san kur’ani kenan na nan. Ya ce amma da yana fargaba.
“To amma da ya ga haka abun ya faranta masa rai duk damuwowinsa da suke damunsa sun fita daga zuciyarsa. Saboda haka ya ce a dalilin wannan jin dadin yake cewa ya karrama wadannan bayanin Allah da suka tsaya tsayin daka wajen koyar da wadannan da sauransu.”
“Ya ce tun da aka masa abun da aka masa a Kaduna bai samu nutsuwa mai dadi ba sai da ya ji karatun yara suna kira’o’u daban-daban da takbili ya ji abun ya masa dadi sosai, saboda dalilin haka, albishir din da ya mana, ya ce, ya yafe wa kowa; duk dan Nijeriya da ma na duniya gaba daya, ya yafe masa in akwai wani abu a tsakaninsu.
“Shi kuma yana rokon in akwai wani da ya masa wani abu yana rokon don Allah a yafe masa. Abun da yake neman ke nan, saboda shi ya ce dukkanin burinsa ya gama cika. Duk abun da yake nema a wajen Allah, Allah ya masa saura guda daya.”
“Don haka ya ce ya riga ya yafe wa duk wani da yake da wani abu a tsakaninsu shi ma na neman hakan saboda yana son ya gamu da Allah lafiya.”
Sayyid Ali ya ya gode wa mahaifinsu bisa hidimar da ya ke yi wa addini. Ya kuma yaba ma wadanda suka rike amana wajen tafiyar da dukkanin amanar da Shehi ya ba su musamman na koyarwa.
Sai ya taya wadanda suka samu karatun murna da cewa za a karramasu da kyautuka daban-daban masu daraja.