Jirgin yakin sojojin saman Nijeriya karkashin rundunar (OPWP) ya tarwatsa sansanin ‘yan ta’adda da ke dajin Yadi a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Kaftin Kabiru Ali ya fitar, ta ce, an kai harin ne a ranar Juma’a, 27 ga watan Satumba, 2024, biyo bayan wasu sahihin rahotannin sirri da ke nuna bayyanar wasu dimbin ‘yan ta’adda da makamansu a dajin Yadi.
- Ba Kare Bin Damo A Wasan Hamayya Na Madrid Derby
- Kashin Shettima Ya Dawo Nijeriya Bayan Taron Majalisar Ɗinkin Duniya Na 79
Ya ce, na’urar leken asiri da sa ido, da bincike ta kara tabbatar da kasancewar ‘yan ta’addan da baburansu a dajin.
Sanarwar ta ce, karin bayanan da aka samu sun nuna cewa, sansanin mallakar fitaccen kasurgunin dan ta’adda ne, Kadaɗe Gurgu, wanda na hannun damar Dogo Giɗe ne.
Ya ba da tabbacin cewa, rundunar sojojin saman Nijeriya tare da haɗin gwiwar sojojin kasa, za su ci gaba da fatattakar ‘yan bindiga tare da wayar da kan jama’a game da halin da ake ciki na yaki da ‘yan ta’addan, ta hanyar sintiri akai-akai, da kuma dakile hare-haren ‘yan bindiga a yankunan.