Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya (NAFDAC) ta gargaɗi jama’a kan wasu allurai da ta gano na jabu.
A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, hukumar ta ce waɗannan allurai ba su da rajistar NAFDAC, amma ana siyar da su a kasuwanni da shagunan magunguna a sassa daban-daban na ƙasar nan.
- Xi: Alakar Sin Da Rasha Ta Zama Misali Na Kyakkyawar Dangantakar Manyan Kasashe
- Gwamna Yusuf Zai Kaddamar Da Majalisar Shurah Ta Jihar Kano
NAFDAC ta ce cikin waɗannan jabun allurai akwai Gold Vision Oxytocin Injection mai ɗauke da lambar rajista ta bogi A4-9566.
An bayyana cewa an haɗa maganin a wani kamfani da ake kira Anhui Hongye Pharmaceutical Co. Ltd da ke ƙasar China, amma kamfanin Gold Vision Medicals da ke Jihar Enug ke yaɗa shi.
Hukumar ta roƙi jama’a su guji amfani da irin wannan allura, tare da yin taka-tsantsan wajen sayen magunguna domin kare lafiyarsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp