Domin kara inganta ayyyukan ta, Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya NAHCON ta kafa kwamiti domin karbar korafa-korarfe daga wadanda suka yi aikin Hajjin bana da kuma wadanda suka gudanar da aiki Umara kuma suna da wani korafi a kan hukumar ko kuma wani ma’aikaci ko kuma bangaren masu ayyuka a karkashin hukumar, dasu gabatar da korafinsu ga hukumar domin daukar matakin gyara a yayin aikin hajjin shekara mai zuwa.
Bayanin haka ya fito ne a takardar sanarwa da hukumar ta buga a wasu jaridun kasar nan, hakan kuma ya biyo bayan wasu korafe-korafe ne wasu masu ruwa da tsaki suka gabatar a kafafen sadarwa na intanet ciki har da Gwmanan Jihar Neja Muhammad Bago, inda ya nemi a rusa hukumar a dawo da harkokin aikin hajji ga jihohi.
- Zai Yi Wahala A Magance Matsalar Tsaro Matukar… – Janar Lagbaja
- Peng Liyuan Ta Yi Kira Da Karin Hadin Gwiwa Tsakanin Kasa Da Kasa Domin Takaita Cututtukan Kanjamau Da Tarin Fuka
Sanarwa ta bayar da wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Agusta 2024 ga duk duk wanda yake da wani tsokaci ko shawarwari na yadda za a kara inganta aikin Hajji da Umara a shekara mai zuwa ya gabatar wa hukumar.
An kuma bukaci duk mai korafi ya rubuta cikakken sunansa da adireshinsa ya kuma aika zuwa hedikwatar hukumar da ke Abuja.
A wani bangaren kuma Hukumar Koli ta Addinin Musulunci (NSCIA) ta bayyana aniyyarta na bincikar Hukumar Aikin ta Nijeriya NAHCON a kan yadda ta gudanar da aikin hajjin bana musamman ganin yadda aka samu korarfe-korafe daga bangarori da dama, musamman daga masu ruwa da tsaki inda suka nuna rasahin gamsuwarsu a kan yadda aka gudanar da wasu lamurrori da suka shafi aikin hajjin bana.
Hukumar ta bayyana wannan shiri nata ne bayan taron da ta gabatar na kwamitin zartarwarta da aka yi a babban dakin taron babban masallacin kasa da ke Abuja ranar Asabar 6 ga watan Yuli 2024.
A takaradar bayan taron da babban sakatarenta, Farfesa Isahak Oloyede ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa, a halin yanzu hukumar na jiran rahoton yadda aka gudanar da aikin hajjin ne daga NAHCON kafin ta fara gudanar da nata binciken da bin diddigin korarfe-korafen da masu ryuwa da tsaki suka gabatar a kan yadda aka gudanar da aikin hajjin bana.
Hukumar wadda ita ce, a kan gaba a cikin kungiyoyin addinin musulunci a Nijeriya ta kara da cewa, “Ganin korafe-korafe daga masu ruwa da tsaki a kan yadda aka gudanar da harkokin da suka shafi aikin hajjin bana, taron ya yanke shawarar a jira fitiowar rahoton NAHCON a kan yadda ta jagoranci aikin hajin bana kafin a fara aikin binciken, an kuma amince da kiran babban taro na kasa domin tattauna lamarin aikin hajjin gaba daya. An kuma nuna bukatar a samar da hanyar tattaunawa a tsakanin gwanmati, NAHCON da kuma kungiyar NSCIA domin samun fahimtar juna a dukkan matakan aikin hajji, ta haka ne al’ummar musulmi musamman alhazai za su amfana da irin gudummawar da gwamnati ke bayarwa a duk shekara a kan aikin hajji.