Hukumar Jin Dadin Alhazai ta kasa, NAHCON ta mayar da Naira 61,080 ga mahajjata 6,239 da suka gudanar da aikin Hajji ta Jihar Kaduna a shekarar 2023.
NAHCON ta bayyana cewa, an mayar da kudaden ne sakamakon katsewar wutar lantarki da aka samu a lokacin da alhazai ke zaman Minna, lamarin da ya sanya na’urorin sanyayawa daina amfani a rumfuna wanda hakan ya haifar da tangarda da bacin rai ga mahajjatan.
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Fashi 40, Sun Ceto Mutum 319 A 2024
- Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Karramawar Da Sojoji Suka Yi Wa Seyi Tinubu
Wata sanarwa da kakakin hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa, kowane mahajjaci zai karbi kudi naira 61,080, kuma za a tura wadannan kudaden ne kai tsaye cikin asusun bankin maniyyatan da abin ya shafa.
Shugaban Hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ya bukaci jami’an hukumar da su tabbatar da bin ka’idojin tabbatar da gaskiya da rikon amana.