Shugaban Hukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya sanar da tsawaita wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025 zuwa ranar 10 ga Fabrairu, 2025.
Karin wa’adin na zuwa ne biyo bayan koke-koke da aka kai wa hukumar na a kara wa maniyyatan da suka gaza kammala biyan kudinsu a kan lokaci.
- Nijeriya Na Iya Fuskantar Ƙarancin Maniyyata A Hajjin Bana
- EFCC Ta Gurfanar Da Manajan Darakta Kan Damfarar ₦144m A Gombe
Farfesa Usman ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da ya gudana a manhajar ‘Zoom’ a ranar Talata 4 ga watan Fabrairu, 2025, tare da masu ruwa da tsaki a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji.
Shugaban Hukumar NAHCON ya yi kira ga Sakatarorin Zartarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jiha da su yi aiki tare da Hukumar don ganin an mika kudaden a kan lokaci, wanda ke da muhimmanci wajen tabbatar da biyan kudin masaukan da aka riga aka bincika kuma aka tanada.