Gabanin fitar da sababbin takardar kudin da aka sauya wa fasali, babban bankin Nijeriya CBN ya yi gargadin cewa zai takaita amfani da tsabar kudi yayin da ya sanya dokar cewa, kololuwar kudin da za a iya fitar wa daga asusun daidaiku shine N20,000 a kullum sai naira N50,000 akan cak na wani mutum da ya bayar.
A baya dai, gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa zai sake fasalin Naira don ganin tattalin arzikin Nijeriya ya habbaka da kashi 100 cikin 100 ta hanyar takaita mu’amala da tsabar kudi.
A yayin da ake kaddamar da sabon fasalin kudin N200, N500 da N1,000, gwamnan ya kuma bayyana cewa za a yi amfani da mafi girman takardun kudin ne a matsayin adana kawai, kananan takardun kudin ne kawai za suyi ta yawo a hannun jama’a.
Dangane da haka, babban bankin a cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 6 ga Disamba, 2022 mai dauke da sa hannun Daraktan CBN, mai Sa ido kan harkokin bankuna, Haruna Mustafa, ya bayyana cewa daga ranar 9 ga Janairu, 2023, naira N200 zuwa kasa ne kawai bankuna za su yi amfani da su a cikin injin bayar da takardun kudi (ATMs).