Gwamnatin Najeriya ta jaddada kudirinta na aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC na shekarar 2024 da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin, inda ta kuma jaddada aniyarta ta yin amfani da sakamakon hadin gwiwar wajen samun ci gaba mai dorewa.
Daraktar sashen kula da yankuna a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Janet Olisa ce ta bayyana hakan a wani taron kaddamar da babban kwamitin hadakar ma’aikatun kasar, a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba. Tana mai cewa, an dora wa kwamitin alhakin sauya yarjeniyoyin fahimtar juna da aka sanya wa hannu a taron FOCAC da kuma ziyarar da shugaba Bola Tinubu ya kai kasar Sin zuwa ayyukan raya kasa na zahiri wadanda za su amfanar da kasar.
Olisa, wanda ita ce shugabar kwamitin, ta bayyana cewa aiwatar da sakamakon zai mayar da hankali ne wajen ciyar da Najeriya gaba a fannonin da suka fi muhimmanci, kamar noma, tattalin arziki na dijital, da samar da muhimman ababen more rayuwa.
Kazalika, mahalarta taron sun jaddada muhimmancin inganta samar da ayyukan yi, da karfafa tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar ’yan Najeriya, ta hanyar kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp