A jiya juma`a 24 ga watan nan ne mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranci bikin aza harsashin ginin masana`antar samar da kayan sarrafa hasken rana, domin samar da wutar lantarki a jihar Nasarawa dake shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya.
Ita dai wannan masana`anta, wadda za ta lashe tsabar kudi har Dala biliyan 71.19, za ta kasance irin ta ta farko a yammacin Afrika baki daya idan har an kammala ta.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin a garin Gora dake jihar ta Nasarawa, mataimakin shugaban kasa Farfessa Yemi Osinbajo ya ce kasancewar jihar ta Nasarawa tana da arzikin sinadaran da ake amfani da su wajen samar da falankin dake zuko hasken rana don sarrafawa zuwa wuta ya sanya gwamnatin tarayyar yanke shawarar kaddamar da wannan gagarumin aiki a jihar.
Ya ce matakin zai taimaka sosai wajen aza Najeriya cikin sahun kasashe makwafta da suke amfani da hanyoyin samar da wuta domin kawo karshen matsalolin dumamar yanayi da gurbatar muhalli.
Aikin kamar yadda mataimakin shugaban kasar ya fada zai gudana ne karkashin kulawar hukumar kirkire-kirkiren fasaha ta Najeriya wato NASENI har ila yau yana daya daga cikin kokarin gwamantin Najeriya wajen tabbatar da ganin ta kara fadada saka jarin ta a fagen samar da makamashi.
Kuma akwai kyakkywan fatan aikin zai iya kawo sauyi mai ma`ana ta fuskar sake fasalin wutar latarki da makamashi a Najeriya.
“Wannan masana`anta zata zo a lokacin da ya dace, inda ban da cin gajiyar ta da jama’a zasuyi, ta zo kuma daidai manufa da shirye shiryen kungiyar tarayyar Afrika ta amfani a sabbin hanyoyin samar da makamashi domin kawo karshen matsalolin dumamar yanayi da gurbatar muhalli, baya ga tasirin da za ta yi wajen kawo saukin farashin na`urorin samar da wuta ta hasken rana a Najeriya”
A nasa jawabin, shugaban hukumar kirkire-kirkiren fasaha ta Najeriya Farfesa Muhammad Haruna cewa yayi tun shekaru goma da suka gabata hukumar ta tsunduma cikin harkar samar da wuta ta amfani da makamashin solar a Najeriya.
“Hukumar NASENI karkashin jagoranci na da kuma gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari sun damu mutuka bisa yanayi wutar lantarki a Najeriya, wannan ce ta sa aka mayar da hankali wajen amfani da kimiya da kirkire-kirkiren fasaha na cikin gida wajen amfani da albarkatun cikin gida domin kawo dauki ga shirin gwamnati na sake fasalta harkokin wuta a kasa” (Garba Abdullahi Bagwai)