Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa kungiyar kwadago cewa nan ba da jimawa ba zai tura kuduri kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa ga majalisar dokoki don amincewa da shi.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a jawabinsa na Ranar Dimokuradiyya a ranar 12 ga Yuni, 2024.
- Mun Fara Aiki Da ‘Yan Bori – Hukumar Tace – Fina-finai
- Tinubu Ya Ba Jama’an Tsaro Umarnin Kamo Ƴan Ta’addan Da Suka Kashe Mutane A Katsina
“Nan ba da jimawa ba za mu aike da kudirin zartarwa ga majalisar dokoki don gabatar da abin da aka amince a matsayin mafi karancin albashi na tsawon shekaru biyar ko kasa da haka,” in ji shugaban.
Kazalika, ya musanta zargin kama shugabannin kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) da kungiyar kwadago (TUC), lokacin da suka gudanar da yajin aiki.
“Maimakon haka, an gayyaci shugabannin kungiyoyin kwadago don tattaunawa da kuma cimma matsaya,” in ji shi.
A gefe daya, Tinubu ya kuma amince da matsalolin tattalin arziki wadanda suka jefa ‘yan Nijeriya cikin tsaka mai wuya.
Ya yi alkawarin ci gaba da gyara game da tattalin arziki domin samar wa ‘yan kasar nan makoma mai kyau.
“Gyare-gyaren da muka kaddamar na da nufin inganta tattalin arziki don samun ci gaba. Babu shakka gyare-gyaren sun haifar da wahala. Amma duk da haka, dole ne a yi su don gyara tattalin arzikin da ya jima yana tafiyar hawainiya.”
‘Yan Nijeriya dai na ci gaba da kokawa kan yadda kayayyakin masarufi ke ci gaba da tashin gwauron zabi, inda suke kira ga gwamnati da yi wani abu don a samu sassauci.