Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya soki Shugaba Bola Tinubu kan yawan rancen da gwamnatinsa ke karɓowa.
Yayin hira da gidan talabijin na Arise TV, Melaye ya tambayi dalilin da ya sa ake ci gaba da karbar rance duk da iƙirarin rage ɓarna.
- Kasar Sin Ta Zama Wurin Da Aka Fi Zaba Domin Warware Takaddamar Cinikayya Da Ta Shafi Kasa Da Kasa
- Kasar Sin Ta Bayar Da Gaggarumar Gudunmuwa Ga Wanzuwar Zaman Lafiya Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya
“Me ya sa shugaban ƙasa ke neman rance na dala biliyan 1.7 daga Bankin Duniya? Me ya sa majalisar dattawa ta amince da fiye da dala biliyan 21, tare da wasu da ake jiran amincewarsu?” in ji shi.
Ya kuma yi suka kan sayen jirgin ruwa da jirgin sama na fadar shugaban ƙasa, yana kiran hakan da rashin kishi.
“Ba abin mamaki ba ne idan shugaban ƙasa ya fara neman rance a wajen Opay da Moniepoint nan gaba,” Melaye ya ƙara da cewa.
Melaye ya kuma yi zargin cewa an ƙara kasafin kuɗin majalisar dokoki don yi wa shugaban ƙasa biyayya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp