Kungiyar kwallon kafa Napoli ta kori Rudi Garcia daga aikinsa na kocin kungiyar, watanni hudu bayan nada shi a matsayin koci.
- BUK Ta Dakatar Da Jarabawa Sakamakon Yajin Aikin NLC Da TUC
- Babu Ranar Daina Amfani Da Tsofaffin Takardun Naira – CBN
Zakarun na kasar Italiya sun sanar da haka a ranar Talata, inda suka bayyana cewar rashin tabuka abin a zo a gani a matsayin dalilin korar Garcia.
Napoli ta kuma bayyana dawowar tsohon kocin ta Walter Mazzarri akan kwantiragin shekara daya.
Maki 10 ne tsakanin Napoli da masu jan ragamar gasar Serie A ta kasar Italiya Inter Milan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp