Ƙungiyar Likitoci ta Nijeriya (NARD) ta nanata cewa, yajin aikin da ta tsunduma ba gudu ba ja da baya a duk fadin kasar har sai an biya buƙatunta 19 da ta gabatar.
Ƙungiyar ta kuma bayyana da’awar gwamnatin tarayya na biyan bashin Naira biliyan 43 a matsayin abin da ba shi da tushe balle makama, tana mai cewa, wani ɗan kasafi ne kaɗan daga cikin kuɗaɗen da kungiyar ta bukata aka bata.
Da yake magana da wakilinmu, Shugaban NARD, Dr. Muhammad Suleiman, ya yi takaicin cewa daga cikin buƙatun ƙungiyar 19, biyu ne kawai – sake duba albashi na kashi 25-35 da kuma alawus ɗin haɗin gwiwa aka aiwatar – yayin da “sauran 17 na nan ba a warwaresu ba.”
“Wannan yajin aikin yana nan yana gudana, har sai an biya duk buƙatunmu mafi ƙaranci,” in ji shi.
NARD ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a duk faɗin ƙasar a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, bayan abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati na cika jerin “mafi ƙanƙancin buƙatunta.” Wannan matakin dai tuni ya riga ya kawo cikas ga ayyuka a asibitoci mallakar gwamnatin tarayya da na jiha a faɗin ƙasar.
A halin yanzu, Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, a cikin wata sanarwa da Shugaban Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Alaba Balogun ya fitar, ya nace cewa, gwamnati ta saki kuɗaɗe kuma tana ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙwadago don ganin an kawo ƙarshen yajin aikin ƙungiyar NARD.














