Kwamishinan yada labarai na jihar Kaduna, Malam Ahmed Mai yaki ya mayar da martani ga nasarar da jam’iyyar APC ta samu a mazabar Dan majalisar wakilai na tarayya ta Chikun/Kajuru inda ya bayyana ta a matsayin sahihancin gwamnatin Gwamna Uba Sani da manufofinta na hada kan jama’a.
Mai yaki yana amsa tambayoyin manema labarai ne bayan bayyana sakamakon zaben mazabar kujerar dan majalisar wakilai na tarayya na Chikun/Kajuru da kuma mazabar Zariya Kewaye da Basawa.
- An Yi Gwaji Na Biyu Na Bikin Tunawa Da Nasarar Sinawa A Yakin Kin Harin Japan
- Daje Na Jam’iyyar APC Ya Lashe Zaɓen Majalisar Dokokin Jihar Neja
Ya ce sakamakon ya nuna irin amincewar al’ummomin da ke Kaduna a yanzu a kan shugabancin Gwamna Uba Sani da kuma jam’iyya mai mulki, inda ya ce nasarar da aka samu “na tarihi ce da kuma alamta nasarorin gwamnatin APC.
Ya bayyana cewa da wannan nasarar da jam’iyyar ta samu a jihar Kaduna, ya kara karfin ikonta zuwa yan kunan da aka ganin kamar suna karkashin ikon jam’iyyar adawa ne.
“A cewar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Jam’iyyar APC ta samu kuri’u 34,580 inda ta lallasa abokan hamayyarta da gaske. Jam’iyyar PDP, wacce a da ake kallonta a matsayin ‘yan adawa a Chikun da Kajuru, ta samu kuri’u 11,491 kacal, yayin da jam’iyyar (ADC) ta samu kuri’u 3,477. Jam’iyyar (SDP) ta biyo baya da kuri’u 142 kacal”
Mai yaki ya alakanta nasarorin da aka samu a kan jagorancin Gwamna Uba Sani wanda ya mayar da hankali a kai, wanda ya samar da kyakkyawan sakamako ta hanyar samar da ababen more rayuwa, sabunta harkokin kiwon lafiya, gyare-gyaren ilimi, da matakan tsaro – manufofin da suka yi tasiri sosai ga masu kada kuri’a da kuma share fagen samun gagarumar nasara.
“Al’ummar Chikun da Kajuru da Zariya Kewaye da Basawa sun yi magana da babbar murya – suna son shugabanci mai ci gaba, ba wai alkawuran da za a sake yin amfani da su ba, sun amince da salon jagorancin Gwamna Uba Sani na hada kai”
Mai yaki ya jaddada cewa jam’iyyar APC ba wai kawai ta karya wani sabon salo ba ne, har ma ta tabbatar da matsayinta na babbar jam’iyyar siyasa a jihar Kaduna.
Ya kara da cewa irin wannan gagarumin nasara da aka samu ya sanya jam’iyyar a kan turbar da ta dace kafin shekarar 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp