Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yabawa bangaren shari’a bisa tabbatar da adalci ga wadanda suka cancanta.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan ukuncin da kotun koli ta yanke wanda ya tabbatar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
- Yaƙin Sudan: Gwamnatin Jigawa Ta Samarwa Dalibanta 194 Guraben Karatu A Jami’o’in Cyprus Da indiya
- Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Aikin Tiyatar Ido Kyauta Ga Majinyata 3,600 A Jihar Kaduna
Gwamna Fintiri ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jaridu jimkadan da yanke hukuncin kotun, ya godewa jama’ar jihar bisa jajircewar da suka nuna wajan tsaya masa tun daga matakin kotu sauraron kararrakin zabe zuwa hukuncin kotun Koli.
Ya ci gaba da cewa “wannan hukuncin yana kara tabbatar da kuri’unku da kuka zabe ni dashi lokacin zaben kujerar gwamna a 2023, na gaskiya ne, wannan nasarar da al’ummarmu ta samu a kotu, nasarace da ke nuna adalcin dimokradiyyar Nijeriya. ” inji Fintiri.
Haka kuma gwamnan ya mika godiya ga mutanen dake masa fatan alheri a fadin kasar nan, tawagar lauyoyin da suka tsaya tsayin daka, domin tabbatar da manufofin dimokuradiyya, ya ce lamarin ya Kara masa kuzari wajen kara kaimin yiwa jama’ar jihar hidima.