Sanata mai wakiltar mazaɓar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi amfani da shafinta na Facebook domin jinjinawa al’ummar mazaɓarta, da al’ummar jihar Kogi, da kungiyar kwadago ta kasa (NLC), da kungiyar lauyoyin Nijeriya, da sauran magoya bayanta da suka tsaya mata a lokacin da majalisar ta dakatar da ita na tsawon watanni shida.
Akpoti-Uduaghan, wacce ta koma ofishinta na majalisar dattawa a ranar Talata bayan da mahukuntan majalisar dokokin kasar suka rufe shi, ta ce nasarar da ta samu sai da aka yi takaddama wajen neman adalci.
‘Yar majalisar ta ce, “Na gode, tafiya ce mai nisa don tabbatar da adalci yayin da muke sabuwar ɗaurin ɗamara don yin hidima da gaskiya da jajircewa wajen sauke nauyin al’ummarmu. Don haka, ina matukar godiya ga mutanen Kogi ta tsakiya, jihar Kogi da kuma Nijeriya baki ɗaya saboda addu’a da goyon bayansu. Wannan ba nasarata ce kaɗai ba, namu ne baki ɗaya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp