Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
Dangane da halin da muka tsinci kanmu na matsin rayuwa, akwai bukatar kawo wasu nau’o’in abinci na gargajiya da suka kamata a rika ci saboda za su taimaka wajen daukar tsawon lokaci ba tare da an ji yunwa ba sai dai kwankwadar ruwa kawai.
Ga nau’o’in abincin kamar haka
Kwadon garin kwaki:
Domin shi garin kwaki idan ka kwadanta shi ka ci ka koshi, to zai zama babu abin da za ka nema in ba ruwa ba.
Abubuwan da za ku tanada domin hadawa:
Garin kwaki, kulikuli, Man Ja ko na Gyada, tumatur, albasa, magi da gishiri.
Yadda za ku hada:
Za ku samu garin ku, Yellow (mai ruwan kwai) mai kyau shi ne ya fi kyawun kwado, sai ku zuba shi a roba sannan ku zuba masa ruwa ya sha kansa, sai ku tsiyaye ruwan tsab ku ajiye shi a gefe, saboda ya sha iska, sannan ku yanka tumatur da albasa, sai ku dan soya manku da albasa ta yadda zai yi kamshi, sai ku dauko kulikulinku wanda dama kun daka shi da kayan hadi, sai ku zuba a cikin garin, ku zuba tumatur da albasar da kuka yanka, ku zuba magi da dan gishiri, sannan ku zuba man da kuka soya sai ku gauraya su gaba daya.
Haba dadi kan dadi kenan, kuma wannan hadin yana matukar rike ciki sosai, ba ya sa mutum ya ji yunwa da wuri sai da mutum ya yi ta shan ruwa.
Ga karin wani hadin:
Fatan Wake:
Abubuwan da za ku tanada:
Wake, tattasai, tumatur, albasa, manja.
Yadda za ku hada:
Da farko za ku dora ruwa a wuta kafin ya tafasa sai ku gyara wakenku ku wanke shi ku zuba a cikin ruwan da kuka dora a wuta ku dan sa masa gishiri kadan, sannan ku saka masa kanwa kadan saboda ya nuna da wuri kar ya ci miku gas idan ya yi rabin dahuwa daman kun gyara kayan miyarku kun nika ko jajjagawa sai ku zuba a cikin waken tare da albasa, daga nan sai ku zuba manja wasu suna soyawa tare da manja sannan su zuba, wasu kuma ba sa soyawa suke zubawa ya danganta da yadda kuke so ku zuba magi, gishiri da kori wasu suna sa karafish wato kifin nan kanana yana kara dadi sai ku barshi ya yi ta dahuwa har ya yi.
Wasu idan za su ci suna jika gari su barbada a ciki soboda ya rike musu jiki sosai kar su ji yunwa da wuri. A ci dadi lafiya.
Mandako:
Shi ma wannan yana rike ciki sosai ba ya sa mutum jin yunwa da wuri.
Abubuwan da za ku tanada:
Rogo, kulikuli da gishiri:
Yadda ake hadawa:
Za ku samu rogo sai ku dafa shi ya dahu sosai sai ku sauke. Sai a daka kulikuli ya yi laushi a sa masa magi, gishiri ya yi dadi, sai a hada su waje daya da rogon a sa a turmi a daka shi kamar sakwara. Sai a ci, Allah ya sa a kammala zanga-zanga cikin aminci, amin.