A yau Litinin, rundunar sojojin ruwan kasar Sin ta bayyana cewa, jiragen sama kirar J-15T, da J-35 da KongJing-600, sun yi nasarar kammala atisayen sauka da tashin farko bisa taimakon wata majaujawar maganadisu mai amfani da wutar lantarki a wani babban jirgin dakon jirage mai suna Fujian.
Nasarar ta nuna cewa, babban jirgin dakon jiragen na farko na kasar Sin da aka kera a cikin gida mai dauke da majaujawa, ya nuna kuzarin taimaka wa tashi da saukar jiragen sama bisa taimakon majaujawar maganadisu, lamarin da ya nuna wata sabuwar nasara da aka cimma a fannin samar da manyan jirage masu dakon jiragen sama na kasar Sin.
A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sashen harkokin sojojin sama na manyan jirage masu dakon jiragen sama na rundunar sojojin ruwan kasar Sin ya kara samun ci gaba cikin hanzari, inda ya samu tagomashi daga amfani da jirgi daya zuwa amfani da tsarin kayayyakin aiki masu yawa, sannan daga tashi da sauka daga sansanin soja a doron kasa zuwa tashi da sauka daga manyan jirage masu dakon jiragen sama, kana daga tashi daga jirgin dako ta hanyar tsalle zuwa bisa taimakon majaujawar maganadisu, kuma har ila yau daga samun damar tashi kawai zuwa fasahar iya gwabza yaki.
Rundunar sojojin ruwan ta kasar Sin na ci gaba da mazayawa sannu a hankali zuwa ga cikar burin zama rundunar da ta kai matakin farko na duniya a bangaren teku. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp