A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana cewa, nauyin dukkanin kasashen duniya ne jan hankalin kasar Japan, game da bukatar kawar da burbushin masu ra’ayin amfani da karfin soji. Yayin taron manema labarai na yau da kullum da ya jagoranta a yau, Guo ya yi kira da a hada karfi waje guda, don kare sakamakon yakin duniya na biyu, da odar duniya ta bayan yakin.
Guo, ya yi tsokacin ne bayan da kasar Sin ta karbi wasu takardu daga kasar Rasha, masu kunshe da shaidu game da ayyukan tawagar sojin Japan mai lamba 731, tawagar da ta rika yin gwajin kwayoyin cututtuka kan al’umma a matsayin matakin yaki a lokacin yakin duniya na biyu.
Takardun sun sake shaida yadda tawagar sojin mai lamba 731, ta aikata muggan laifukan cutar da bil’adama, kuma sun samu goyon bayan wasu shaidun na daban da ba za a iya musantawa ba.
Guo, ya kara da cewa, wani abu mai tayar da hankali shi ne, duk da tarin shaidun da ake da su, sassan ’yan ra’ayin-rikau na kasar Japan, da gangan sun ci gaba da karyatawa, da rage muhimmancin batun, ko yiwa ta’asar da kasar ta tafka, da muzgunawa bil’adama kwaskwarima. (Saminu Alhassan)














