Lokacin Da Ya Kamata A Girbe Shi:
Ana girbe shi bayan ya gama girma baki-daya, sai dai; ya danganta da nau’in Irin da aka shuka, haka nan bayan an girbe shin, ana iya samun daga tan kimanin 70 zuwa tan 80.
Sayar Da Shi:
Mai noman sa, zai iya sayar da shi ga ‘yan kasuwar da ke sana’arsa sayar da shi ko a manyan shaguna da gidajen sayar da abinci ko a Otel ko kuma ya yi tallansa a kafar yanar gizo.
Adana Shi:
Kabeji ya fi saurin girma a ma’aunin yanayin da ya kai daga kimanin 55 zuwa 60, inda kuma akwai nau’ikansa da ke saurian girma a ma’aunin yanayin da ya kai daga 20 zuwa 25.
Nomansa ya samo asali ne daga farkon kafuwar kasar Girka da kuma a kasar Romaniya, inda nomansa ya ci gaba da yaduwa zuwa kasar Birtaniya ya kuma yadu zuwa sauran wasu kasashe.
Akasari a Nahiyar Afirka, musamman a Nijeria ana yawan yin amfani da shi, musamman a lokatan bukukuwan Sallah ko na Kiristimeti da sauransu, ya kuma kasance yana dauke da sinadarin ‘calcium’ da ke inganta lafiyar jikin Dan’adam.
Bugu da kari, nomansa ba shi da wata wahala; kuma akwai sauki wajen kula da shi bayan an shuka shi, inda kuma ba sai ka na da kudade da yawa ba; za ka iya fara nomansa, ko a bayan dakinka za ka iya yin nomansa.
Gyaran Gona:
Ana iya shuka shi a kan kowace irin kasar noma, inda ake bukatar bayan manominsa ya yi gyaran Gona, sai ya shuka Irin nasa, haka manominsa zai iya yin amfani da Tarakta; don gyaran gonar, musaman idan kasar noman na da tsauri; sai ya yi mata haro, daga nan kuma sai ya shuka Irin.
Shuka Shi:
Ramin da za ka shuka Irinsa, ana so ya kai zurfin kafa daga 2 zuwa 3, idan kuma za ka yi renon Irin ne, ana so ka saka shi a cikin buhu ko cikin ledar da ake yin renon Iri, bayan sati uku zuwa hudu sai ka canza masa wani gurin; bayan ya kai tsawon santi mita 14 zuwa santi mita 16.
Ban Ruwa:
Ana so a dinga yi masa ban ruwa akai-akai a duk sati, ganin cewa Kabeji na bukatar ruwan da ya kai santi mita 3.8, musamman ganin cewa Kabeji ba ya son yanayi na irin na fari.
Zuba Taki:
Ana so tun farkon lokacin da aka shuka Irinsa, a zuba masa takin zamani, musamman don ya yi saurin girma, inda kuma bayan sati uku da canza masa wani gurin; ana so a kara zuba masa wani takin.
Kare Shi Daga Kamuwa Da Cututtuka:
Kamar sauran amfanin gona, shi ma Kabeji akwai cututtukan da suke yi masa illa; kamar wadanda ake kira a turance, ‘Flea beetles’ da sauran makamantansu.