Ta iya yiwuwa sauyin yanayi ne kan sa, Kajinka na gidan Gona ke ke yin ƙananan Ƙwai, saɓanin yadda na maƙwabcinka ke yin manya-manyan Ƙwai.
A saboda haka, ya kamata ka yi ƙoƙarin gano waɗane dalilai ne ke haifar maka da wannan matsala a gonarka, musamman domin ƙoƙarin magance ta. Ƙwararru a wannan fanni, sun jero jeren wasu daga cikin dalilan da suka sa wasu masu kiwon Kajin ke samun ƙananan Ƙwai, wasu kuma ke samun manya-manya.
- Shugaba Xi Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev
- Yunwa Ta Kazanta A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Tun Bayan Da Majalisar Dinkin Duniya Ta Dakatar Da Ayyukanta
A matsayinka na sabon mai fara kiwon Kajin gidan Gona, yana da kyau ka san waɗannan dalilai, matuƙar kana buƙatar kajinka su riƙa yin manya-manyan Ƙwai.
Ƙwararre a fannin kiwon Kajin gidan gidan gona, Dakta James Baba Wagati, ya zayyano matakai uku da za su sanya Kajin gidan Gona riƙa yin manya-mayan Ƙwai.
1- Shekaru Da Jinsin Jini:
Wani lokacin, yanayin shekaru da Jinsin Jini ne ke fayyace irin girma ko ƙantantar Ƙwan da Kajin za su yi.
2- Wajen Kwana:
Kajin na buƙatar a tabbatar da ana samar musu da wadataccen ruwan sha a ɗakunan kwanansu da kuma ba su kariya daga kamuwa da cutuka da rage musu wahala da cunkoso da kuma zafi, wanda hakan na iya shafar Ƙwan da za su yi kai tsaye.
3- Abinci Mai Gina Jiki:
Ciyar da su abinci mai gina jiki, wanda ke ɗauke da sinadaran ‘protein, amino acids’, waɗanda za su sanya su yi nauyi tare kuma da buƙatar a riƙa yi musu allurar ƙara musu lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp