Akwai matukar sauki wajen fara noman kayan lambu a Nijeriya, domin kuwa a iya fara noman kayan lambun a ‘yar karamar gona, musamman wajen noman Alayyahu, Tumatir da sauran makamantansu, sannan za ka iya fara yin wannan noma na kayan lambu a bayan dakinka .
Har ila yau, za ka iya shuka kayan lambunka don amfani da shi a gida ko samun riba; sai ka tsara a rubuce yadda za ka yi noman musamman don sanin irin ribar da za ka samu da kuma cin nasara.
- Birnin Beijing Zai Kara Yawan Lambunan Shakatawa
- An Kashe Dorinar Ruwa A Jihar Kebbi Bayan Ta Kashe Mai-Gadin Lambun Basarake
Kafin ka shiga cikin fannin, ya kamata ka san da me za ka fara; kadan ko da yawa? Idan za ka yi mai yawa ne, sai ka dauko hayar ma’aikata su kula maka da noman, don kauce wa yin asara.
Kazalika, ana bukatar ka san wane irin kayan lambu mutanen da ke yankinka suka fi bukata, misali; a Jihar Akwa Ibom, akasarin al’ummar jihar, sun fi bukatar ganyen Ugu.
Kayan Lambun Da Suka Fi Kawo Kudaden Shiga A Nijeriya:
Kowane nau’in kayan lambu, ya danga da wurin da za a yi nomansa; sannan ya danganta da bukatar da ake da ita a yankin da za a noma shi. Domin kuwa, za a iya sayen Iri na Naira 5,000 a shuka gona a kuma kashe kimanin Naira 10,000; wajen ba shi kulawa, inda a cikin ‘yan satuttuka za a iya samun Kudaden shiga masu yawan gaske.
Noman Kayan Lambu Na Rani:
Za a iya samun Kudaden shiga har sau uku a lokacin noman kayan lambu da rani, sai dai; manoma ‘yan kalilan ne ke yin noman rani a Nijeriya.
Haka nan, idan za a fara yin noman kayan lambu a da rani, ana so a tanadi kayan ban ruwa tare da tanadar ingantaccen Irin da ke jure wa kowane irin yanayi da kuma bijere wa harbin kwari ko kuma cututtukan da ke harbin amfanin gona da kuma tanadar rijiyar burtsatse