Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin ta fitar da wani sabon rahoto kan biyayyar Amurka ga ka’idojin hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, wanda ya bayyana cewa, cikin sama da shekara 1 da ta gabata, Amurka ta ci gaba da yin gaban kanta wajen daukaka takunkumai da daukar matakan wariya akai-akai da kara daga shingen haraji, lamarin dake haifar da kalubale mai tsanani ga tsarin cinikayya tsakanin bangarori da kasa da kasa. Dangane da abubuwan dake cikin rahoton, kafar yada labarai ta CGTN ta kasar Sin, ta gudanar da wani nazarin jin ra’ayin jama’a a fadin duniya, wanda ya nuna cewa, kaso 90.53 na wadanda suka bayar da amsa, sun soki jerin matakan da Amurka ke yin gaban kanta wajen dauka da kuma matakan kariyar cinikayya, inda suka yi ammana cewa, matakan sun yi matukar take ka’idojin WTO.
Duk da cewa WTO ta bayyana cewa aya ta 301 ta dokar haraji ta Amurka, ta keta ka’idojinta, Amurka ta ci gaba da yi watsi da ka’idojin hukumar tare da nacewa wajen daukar matakai bisa radin kanta. A watan Afrilun 2024, Amurka ta kaddamar da bincike na aya ta 301 kan masana’antun jigila da ayyukan teku da kera jiragen ruwa na kasar Sin. Cikin nazarin na CGTN, kaso 94.31 na wadanda suka bayar da amsa, sun soki Amurka saboda rashin girmama ka’idojin WTO.
CGTN ta fitar da sakamakon nazarin ne a dandamalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci.
Sama da mutane 6,000 ne suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha)