“Kowacce mace tauraruwa ce a sabon tafarkin zamanantar da kasar Sin,” wannan wani furuci ne da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi cikin jawabinsa na bude taron mata na kasa da kasa na duniya a Beijing.
Wani nazari da kafar yada labarai ta CGTN ta Sin ta gudanar da ya shafi mutane 7292 a fadin kasashe 38, ya nuna yadda jama’a suka amince da rawar da mata ke takawa a matsayin mai muhimmanci wajen ingiza ci gaban tattalin arzki da zaman takewa, tare da nuna yadda aka amince da wannan ra’ayi da kuma nasarorin da aka samu wajen raya harkokin da suka shafi mata a kasar Sin.
Saboda namijin kokarin da aka shafe lokaci mai tsawo ana yi, an samu manyan nasarori da sauye-sauye a harkokin da suka shafi mata a kasar Sin. Kasar ta yi nasarar fatattakar talauci da ba a taba gani ba a tarihi. Haka kuma, tun daga shekarar 1995 zuwa yanzu, an samu raguwar mace-macen mata masu juna biyu da kusan kaso 80. A yau, mata a kasar Sin suna taka muhimmiyar rawa a bangarorin raya tattalin arziki da zaman takewa. Su ne kuma suka dauki kaso 40 na ma’aikata da sama da kaso 60 na wadanda suka lashe lambobin yabo yayin gasannin 4 na wasannin Olympics na lokacin zafi.
Dangane da gamsuwa kan nasarorin da Sin ta samu a bangaren raya harkokin mata, kaso 72.8 na masu bayar da amsa a nazarin daga kasashe maso tasowa, sun yaba da kokarin Sin na horar da mata sana’o’i da tallafawa raya harkokin da suka shafe su. Game da nasarorin da aka samu a kasar Sin wajen shigar mata cikin harkokin raya tattalin arziki da zaman takewa da al’adu, da ma gudunmuwar kasar ga raya harkokin mata a duniya, wadanda suka bayar da amsa daga nahiyoyin Afrika da Asia da kudancin Amurka, sun bayyana gamsuwa matuka.
Kafar yada labarai ta CGTN da jami’ar Renmin ta Sin ne suka gudanar da nazarin wanda ya shafi muhimman kasashe masu ci gaba da ma kasashe masu tasowa. Sun gudanar da nazarin ne ta hannun cibiyar bincike kan harkokin kasa da kasa a sabon zamani. (Fa’iza Mustapha)