Wani rahoto da hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar Talatar nan ya nuna cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin yanayi na daidaito da bunkasuwa yadda ya kamata, kana baki dayan karfin kasar ya inganta matuka, haka kuma tasirinsa a duniya yana karuwa a kai a kai.
Daga shekarar 2013 zuwa 2021, GDPn kasar Sin ya karu da kashi 6.6 bisa dari a duk shekara, wanda ya zarce matsakaicin karuwar kashi 2.6 cikin 100 a duniya, da kashi 3.7 cikin 100 na kasashe masu tasowa a makamancin wannan lokaci. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)