Hukumar Kula da Kididdiga ta Kasa wato NBS, a cikin wasu alkaluman da ta fitar sun nuna cewa, a watan Yulin shekarar 2025 hauhawan farashin kaya a kasar ya ragu da kaso 21.88 idan aka kwatanta da rasuwar farashin a watan Yunin na 2025, wanda ya kai kaso 22.22.
Kazalika, alkaluman sun nuna cewa, a watan na Yulin na 2025 hauhawar ta ragu da kaso 0.34 idan aka kwatanta da na watan Yunin na 2025.
- EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
- Faretin Sojoji Da Sin Za Ta Gudanar Zai Shaida Muhimmancin Zaman Lafiya Da Goyon Bayan Gaskiya Da Adalci Tsakanin Kasa Da Kasa
Bugu da kari, hauhawar farashin kayan abinci a watan Yulin 2025 ya kai kaso 22.74 wanda hakan ya nuna cewa, ya ragu da kaso 16.79 idan aka kwatanta da kaso 39.53 da aka samu a watan Yulin 2024.
Alkaluman sun bayyana cewa, wannan gwagwabar ta wannan raguwar farashin na kayan abinci ta faru ne, saboda sauyin da aka samu na juyin shekara.
A cewar alkaluman daga wata zuwa wani watan, farashin kayan abinci a watan Yulin 2025 ya kai kaso 3.12 wanda kuma ya ragu da kaso 0.14 idan aka kwatanta da kaso 3.25 a watan Yunin shekarar 2025.
Hukumar ta NBS ta kara da cewa, an kuma samu raguwar farashin man girki da na Farin Wake da Shinkafar da ake nomawa a kasar da Nasarar da Fulawa da Dawa da Alkama da sauransu.
Hakazalika, daga shekara zuwa shekara, farashin ya karu zuwa kaso 11.52 a watan Yulin 2025 idan aka kwatanta da kasokaso 33.40 a watan Yulin 2024.
Hukumar ta NBS ta ci gaba da cewa, wannan ya nuna cewa, a watan Yulin 2025, an samu raguwar da wacce aka samu duk dai a irin wannan watan na Yulin 2024 koda yake dai,Hukumar ta kara da cewa, akwai can banbanci, kan wanda aka samu a watan Disambar 2009.
Kazalika, alkaluman sun bayyana cewa, a watan Yulin shekarar 2025, hauhawar daga wata zuwa wani watan ta kai kaso was 1.99,wanda hakan ya nuna cewa,hauhawar ta ragu zuwa kaso 0.31 idan aka kwatanta da kaso 1.68 da aka samu a watan Yulin 2025.
Wannan ya nuna cewa, karuwar farashin na kayan da aka samu a watan Yulin 2025, ta fara wacce aka samu a watan Yunin shekarar 2025.
Hakazalika, a watan Yulin 2025 farashin kayan abinci ya kai kaso 22.74 inda kuma a watan Yulin 2025, aka samu raguwar kaso 16.79 ke nuna cewa idan aka kwatanta da karuwar da aka samu ta kaso, 39.53 a watan Yulin in July 2024.
Hukumar ta bayyana cewa, raguwar farashin na kayan abinci daga wata zuwa wata, mussaman a watan Yulin 2025 ya kai kaso 3.12 inda kuma kuma ya kara yin kasa zuwa kaso 0.14 idan aka kwatanta da na watan Yulin 2025 wanda ya kai kaso 3.25.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp