Shugabar kamfanin jaridar LEADERSHIP, Misis Zainab Nda-Isaiah, ta yaba wa uwargidan shugaban kasar Nijeriya, Sanata Remi Tinubu, bisa jajircewarta wajen inganta rayuwar marasa galihu a fadin kasar nan.
Misis Zainab ta yi wannan yabon ne a lokacin da ta jagoranci tawagar shugabannin gudanarwar kamfanin a ziyarar ban girma ga uwargidan shugaban kasa a fadar gwamnati da ke Abuja.
- Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Tare Da Kwato Makamai A Kano
- Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Zababbun Shugabannin Gabon Da Ecuador
A cewar wata sanarwa da mai taimaka wa uwargidan shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Busola Kukoyi, ta fitar a ranar Talata, Nda-Isaiah ta yi nuni da cewa, ta na lura da irin ayyukan jin-kai da Sanata Tinubu ke yi a fadin kasar nan, don haka, ya dace a nuna godiya ta gaske ga hidimar da ta ke yi a matsayinta na “Uwa ga ‘yan Kasa.”
A yayin ziyarar, mataimakin shugaban kamfanin LEADERSHIP Mike Okpere, ya bayyanawa uwargidan shugaban kasa irin ayyukan agaji da Kamfanin LEADERSHIP ke gudanarwa tare da yin fatan hada hannu da shirin tallafin fata na gari ‘Renewed Hope Initiative (RHI)’ da nufin karfafawa mutane 1,000 da ayyukan yi.
A cewar Okpere, shirin zai mayar da hankali ne wajen samar da sana’o’in dogaro da kai a sassa daban-daban na tattalin arziki da suka hada da rini, kamun kifi, dinki da dai sauransu.
Ya yi nuni da cewa, manufar ita ce a taimaka wa daidaikun mutane su samu ‘yancin cin gashin kansu da kuma zama masu amfani a cikin al’umma.
Uwargidan shugaban kasar, wacce ta yi marhabin da shirin tallafin, ta kuma bai wa tawagar tabbacin yin hadin gwiwa da LEADERSHIP, musamman a fannonin da suka shafi karfafawa da kuma ci gaba mai dorewa.
Yayin da take nuna jin dadinta kan wannan ziyara da kuma irin goyon bayan da LEADERSHIP ke bayarwa a tsawon shekaru, Sanata Tinubu ta bayyana cewa, aikin taimakawa da tallafa wa ‘yan Nijeriya ba gwamnati ce kadai za ta iya yi ba, sai dai tare da hadin kan ‘yan Nijeriya baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp