Hukumar NDLEA da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya ta kai samame wani gida a Unguwar Lekki Jihar Legas inda ta bankado boyayyun miyagun ƙwayoyi.
Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter, ya ce an gano ƙwayoyin Tramadol guda miliyan 13 masu nauyin miligram 225 a gidan .
- Yaki Da Miyagun Kwayoyi: Za A Saya Wa NDLEA Motoci Masu Sulke
- NDLEA Ta Kama Kwalaben Kayan Maye Da Akuskura A Jihar Kano
Femi ya ce gidan babu wani mutum da ke zaune a ciki, sai waɗannan ƙwayoyi da aka ajiye a ciki wanda tuni NDLEA ta kama wanda ake zargi da ajiye ƙwayoyin.